Ogbonnoya Onu yace APC za ta kawo Kudu masu Gabas a zaben 2023

Ogbonnoya Onu yace APC za ta kawo Kudu masu Gabas a zaben 2023

Ministan kimiyya da fasaha a Najeriya, Dr Ogbonnaya Onu, ya fito ya bayyana cewa jam’iyyar APC mai mulki ce za ta lashe zaben 2023 a yankin kasar Kudu maso Gabas idan lokacin zaben yayi.

Ogbonnaya Onu yace duba da yadda jam’iyyar ke da dinbin Magoya baya da kuma goyon-bayan da APC ke samu a kasar Ibo a halin yanzu, babu abin da zai hana jam’iyyar lashe zaben Najeriya mai zuwa nan da kusan shekara 4.

Onu yake cewa ko da dai APC ba ta samu wasu kuri’un kirki a Mutanen yankin Kudu maso Gabashin kasar, a shirya su ke da su marawa APC baya sosai a zaben 2023. Daily Trust ta rahoto mana wannan labari a jiya Litinin.

KU KARANTA: Buhari yayi magana a kan yadda zai raba kujerun Ministoci

Ogbonnoya Onu yace APC za ta kawo Kudu masu Gabas a zaben 2023
Dr. Ogbonnoya Onu ya fara hangowa APC nasara a 2023
Asali: UGC

A jawabin da babban Ministan ya gabatar wajen wani taro da mutanen Kudu maso Gabashin kasar su ka shirya a Garin Ebonyi, Onu yabawa irin kokarin da mutanen yankin su kayi na fitowa su zabi jam’iyyar APC mai adawa a jihar.

Ministan ya kara da cewa, goyon bayan da APC ta samu a bana, ya zarce abin da ta samu a lokacin zaben 2015. SDr. Onu ya bayyana cewa yana sa rai APC za ta doke kowa a yankin, a zaben 2023 kamar yadda abubuwa ke nunawa.

Babban Ministan kasar ya ji dadin yadda ‘Yan Najeriya su ka sake zaben shugaban kasa Muhammadu Buhari a karo na biyu domin cigaba da ayyukan alherin da gwamnatin sa ta yi a cikin shekaru 4 da yayi a kan karagar mulki.

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Asali: Legit.ng

Online view pixel