Gobara Ta Kona Dukiya Mai Yawa a Kasuwar Balogun, ’Yan Kasuwa 86 Sunyi Babbar Asara

Gobara Ta Kona Dukiya Mai Yawa a Kasuwar Balogun, ’Yan Kasuwa 86 Sunyi Babbar Asara

  • Shugaban hukumar bada agajin gaggawa ta kasa NEMA, Ibrahim Farinloye, ya tabbatar da aukuwar gobara a Legas
  • Jami'in ya bayyana cewa har yanzu ana cikin rudani a kan musabbabin tashin gobarar da ta rutsa kasuwar Balogun
  • 'Yan kasuwar sun shiga damuwa kasancewar sun yi anfani ne da bashin banki wurin sayo kayan da gobarar ta cinye

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

A ranar Litinin da ta gabata ne gobara ta lalata wasu kayayyaki na biliyoyin nairori a wasu shaguna a kasuwar Balogun da ke Legas.

Gobara a Bologun Market dake Lagos
Gobarar ta cinye manyan shaguna a layin masu sayar da kayan kwalliya. Hoto: Lagos State Fire Service Asali: Facebook
Asali: Facebook

Gobarar ta kone kayan sashen sayar da kayan kwalliya na babbar kasuwar.

Jaridar Daily Trust ta ruwaito cewa shagunan da gobarar ta shafa suna kan titin Issah Williams, kusa da titin Breadfruit.

Kara karanta wannan

Tuhuma kan aikata laifuffuka 26, Emefiele ya isa kotu, ya gurfana gaban alkali

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Kokarin kashe gobara a kasuwar Balogun

Jami’an agajin gwamnatin jihar da na tarayya sun yi aiki na tsawon sa’o’i ba tare da gajiyawa ba wajen shawo kan gobarar.

Cikin kokarin al'umma da jami'an kashe gobarar, an samu nasarar shawo kan gobarar da misalin karfe 4 na yamma.

Adadin asarar da gobarar ta jawo

Ibrahim Farinloye, shugaban hukumar bada agajin gaggawa ta kasa NEMA a shiyyar kudu maso yamma, ya tabbatar da faruwar lamarin.

Ya ce gobarar ta cinye manyan shaguna guda 20, da dakunan ajiya guda uku, da kuma kanan shaguna guda 16 da ke cikin wani bene mai hawa uku.

A jimlace, Ibrahim Farinloyeya shaida cewa hasarar ta shafi ‘yan kasuwa kusan 86.

Musabbabin tashin gobarar

Farinloye ya bayyana cewa har yanzu ba a san ainihin musabbabin tashin gobarar ba, amma akwai ishara da shugabannin kasuwar suka nuna game da yawan amfani da injinan wutar lantarki a cikin kasuwar.

Kara karanta wannan

“Bamu hana ka murabus ba”: Kungiyar kwadago ta fusata, ta tura sako mai zafi ga Peter Obi

Wasu daga cikin 'yan kasuwar kamar Alhaja Kemi Gbajumo, Iya Oloja, Prince Adewunmi Balogun da Baba Oja sun bayyana matukar alhininsu kan hasarar da gobarar ta jawo.

Sun ce a baya-bayan nan da dama daga cikin ‘yan kasuwar sun cika shagunansu da kaya ne ta hanyar amfani da bashin banki, kuma ba tare da inshora ba.

Saboda haka suke ganin lalle zasu fuskanci kalubale sosai wajen murmurewa daga wannan mummunar hasara da sukayi.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng