Hadarin Mota Ya Hallaka Mutane, Wasu 21 Sun Jikkata Ana Shirin Bikin Sallah

Hadarin Mota Ya Hallaka Mutane, Wasu 21 Sun Jikkata Ana Shirin Bikin Sallah

  • Jami'ar hulda da jama'a ta hukumar kiyaye hadura ta kasa ce ta bayyana faruwar haduran
  • Ta ce haduran sun faru ne a wurare mabambanta kuma sun afka ga mata da kananan yara
  • Kamar yadda labari ya zo mana a yau, ta kuma bayyana manyan dalilan da suka jawo haduran

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Mutane shida ne ciki har da mata da kananan yara suka rigamu gidan gaskiya a wasu jerin haduran mota a jihar Ogun.

Road safety
Hukumar kiyaye hadura ta kasa ta ce tukin ganganci ne sanadin hadarin. Hoto: Federal Road Safety Corps Asali: Facebook
Asali: Facebook

Mutane akalla 21 ne suka jikkata yayin da motocin suka yi karo da juna a kan hanya.

Wuraren da haduran suka faru

Kara karanta wannan

An Samu Sabani a NNPP Saboda Sabuwar Alamar Jam'iyyar da Kwankwaso ya Kaddamar

Jami'ar hulda da jama'a ta hukumar kiyaye hadura ta kasa reshen jihar Ogun, Florence Okpe, ce ta bayyana wuraren da haduran suka faru.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

A cewar ta, hadarin farko ya faru ne a wajejen Fidiwo da misalin karfe hudu na safe.

A hadarin farkon, mutum hudu ne hadarin ya afka da su inda biyu suka mutu biyu kuma suka jikkata.

Ta ce hadari na biyu kuma ya faru ne akan titin Ore-Ijebu-Ode da misalin ƙarfe biyar na safe.

Mutum 20 ne hadarin ya ritsa da su inda mutum 17 suka samu raunuka., yayin da mutum uku suka mutu, biyu maza, da yarinya mace guda daya.

A cewar ta, hadari na ukun ma ya afku ne akan titin Ore-Ijebu-Ode din da misalin karfe biyu na safe.

Hadarin ya afka wa mutum 29 ne yayin da motoci guda biyu suka yi karo.

Kara karanta wannan

Sauyin yanayi: Tsofaffin ma'aikata da matasa 10,000 za su samu aiki da gwamnatin tarayya

Mutane biyu ne suka jikkata a hadarin yayin da na miji daya kuma ya rigamu gidan gaskiya.

Dalilin faruwar hadarin

Jaridar Daily Trust ta ruwaito jami'ar hulda da jama'a na hukumar kiyaye hadura ta kasa tana bayyana dalilin faruwar hadarin.

Jami'ar ta jingina faruwar haduran da gudu mai yawa da kuma gajiya daga ɓangaren matukan motocin.

Yadda hadarin ya hallaka rayuka a Ogun

Kimanin mutane 6 ne suka rasa rayukansu a sanadiyar wani hadarin mota da ya faru akan babbar hanyar jihar Legas zuwa jihar Ibadan.

Hadarin ya faru ne a yayin da wata motar haya kirar Nissan Quest, mai lamba FKJ 297 AJ, dake tahowa daga jihar Legas, ta shige cikin wata babbar mota kirar Iveco, mai lamba LND 902 XE.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng