Yadda wani hadarin mota yayi sanadiyar rayuka 6 a jihar Ogun

Yadda wani hadarin mota yayi sanadiyar rayuka 6 a jihar Ogun

- Mutane 6 sun rasa rayuwankansu

- Hadarin mota ne ya hallaka mutum 6

- Tukin ganganci da rashin kulawa ne ya janyo hadarin

Kimanin mutane 6 ne suka rasa rayuwankansu a jiya ne 17 ga watan Yuli, sanadiyar wani hadarin mota da ya faru akan babbar hanyar jihar Legas zuwa jihar ta Ibadan.

Kakakin masu kula da hurda-hurdar rage cinkuso a manyan titunan mota wato Traffic Compliance Enforcement Corps (TRACE), Babatunde Akinbiyi ne ya tabbatar da faruwar wannan hadari.

Yadda wani hadarin mota yayi sanadiyar rayuwaka 6 a jihar Ogun
Yadda wani hadarin mota yayi sanadiyar rayuwaka 6 a jihar Ogun

Yace hadarin ya faru ne a yayin da wata motar haya kirar Nissan Quest, mai lamba FKJ 297 AJ, dake tahowa daga jihar Legas, ta shige cikin wata babbar mota kirar Iveco, mai lamba LND 902 XE.

KU KARANTA: Ba sai da khaki ba: Idan Shugaban Kwastam ya ga dama ya sa 'yar shara...-Inji Saraki

Babatunde ya bayyana cewa hadarin faru ne sanadiyar gudu na fitar hankali da rashin kulawa da direban karamar motar yake yi. Yace tuni ma’aikatan nasu da na masu kulawa da duk wata alaka ta titin mota wato Federal Road Safety Corps (FRSC) suka kawo dauki da rage cinkoso akan babban titin, tuni mutum 6 sun rasa rayukansu wanda ya hadar da direban karamar mota.

Ya kara da cewa an mika gawarwakin wadannan mutane 6 zuwa babban asibitin koyararwa na Olabisi Onabanjo University Teaching Hospital (OSUTH) a Shagamu.

https://business.facebook.com/naijcomhausa/#

https://twitter.com/naijcomhausa

Asali: Legit.ng

Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng

Online view pixel