Kwamishina Ya Shiga Matsala Yayin da Gwamnan APC Ya Kafa Kwamitin Binciken Tallafin Ramadan

Kwamishina Ya Shiga Matsala Yayin da Gwamnan APC Ya Kafa Kwamitin Binciken Tallafin Ramadan

  • Gwamnatin Jigawa a karkashin Gwamna Umar Namadi ta kafa kwamitin bincike kan abin da ya faru a shirin ciyarwa na Ramadan
  • Kwamishinan yaɗa labarai, Sagir Musa, ya ce za a gudanar da bincike ne kan zargin karkatar da kuɗaɗen shirin a karamar hukumar Babura
  • A ranar Jumu'a da ta gabata ne Gwamna Namadi ya dakatar da kwamishinan kasuwanci kan zargin hannu a wawure kuɗin taimakon talakawa

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Jigawa - Majalisar zartarwar jihar Jigawa karkashin jagorancin Gwamna Umar Namadi ta fara ɗaukar matakai domin gano rashin gaskiyar da aka yi a shirin ciyarwa na watan Ramadan.

Majalisar zartaswar (SEC) ta kafa kwamitin mutum shida da zai gudanar da bincike mai zurfi kan yadda aka aiwatar da shirin na tallafawa mabuƙata a Ramadan a ƙaramar hukumar Babura.

Kara karanta wannan

Gwamna ya naɗa matashi ɗan shekara 37 a matsayin sabon mataimakin gwamna

Gwamna Umar Namadi.
Gwamnatin Jigawa ta ɗauki matakin zaƙulo marasa gaskiya a ciyarwar Ramadan Hoto: Umar Namadi
Asali: Facebook

TABLE OF CONTENTS

Kwamishinan yaɗa labarai, matasa, wasanni da al'adu na Jigawa, Sagir Musa, ne ya bayyana haka a wata sanarwa ranar Litinin, kamar yadda Daily Trust ta ruwaito.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ya ce rahoton farko da kwamishinan ayyuka na musamman ya gabatar a gaban SEC ya nuna cewa an kashe N2.1m a shirin ciyarwa lokacin buɗa baki.

Kwamishinan yaɗa labaran ya ce an bai wa kwamitin wa'adin kwanaki bakwai ya gama bincike kuma ya miƙa rahoton abin da ya gano ga majalisar SEC.

Waɗanda aka sanya a kwamitin

Ya ce kwamitin ya ƙunshi shugaban ma’aikata a matsayin shugaba da kwamishinonin ayyuka na musamman, shari’a, noma, da yada labarai, a matsayin mambobi.

Musa ya ƙara da cewa sakataren watsa labarai na mai girma gwamna zai yi aiki a matsayin sakataren kwamitin, kamar yadda Ripples Nigeria ta ruwaito.

Kara karanta wannan

Karin kudin wuta: Kano da sauran jihohi 12 da suka shirya inganta wuta ga al'ummarsu

Gwamna ya dakatar da kwamishina

Idan ba ku manta ba Gwamna Namadi ya dakatar da kwamishinan kasuwanci, Alhaji Aminu Kanta, bisa zargin karkatar da kuɗaɗen da aka ware domin ciyar da mabuƙata a Ramadan a Babura.

Gwamnatin Jigawa ta ce dakatarwar ta fara aiki nan take a ranar Jumu'a har sai kwamitin binciken da gwamna ya kafa ya gama aikinsa ya miƙa rahoto.

A cewar gwamnatin, matakin da gwamnan jihar ya dauka na daga cikin kokarinsa na tabbatar da bin doka da oda da kuma tafiyar da kudaden gwamnati bisa gaskiya da riƙon amana.

Godwins ya koma PDP kan abu 1

A wani rahoton na daban Mataimakin gwamnan jihar Edo, Omobayo Godwins, ya faɗi alkawarin da aka masa wanda ya sa ya sauya sheka daga LP zuwa PDP.

A ranar Litinin, 8 ga watan Afrilu, 2024 aka rantsar da Godwins a matsayin sabon mataimakin gwamnan jihar Edo bayan tsige Philip Shaibu.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262