Kotu Ta Ci Tarar Jarumar Fina Finai N10m Kan Ɓatanci Ga Malamin Addini a Kafar Sadarwa

Kotu Ta Ci Tarar Jarumar Fina Finai N10m Kan Ɓatanci Ga Malamin Addini a Kafar Sadarwa

  • Kotu ta dauki mataki kan jarumar Nollywood, Halima Abubakar bayan ta ci mutuncin Fasto Johnson Suleman
  • Babbar Kotun Tarayya da ke Abuja ta ci tarar jarumar har N10m tare da bata umarni ta janye kalamanta da ta yi kan malamin
  • Tun farko Fasto Suleman ya zargi Halima da bata masa suna a shafinta na Instagram inda ta kira shi da mugu kuma mayen mata

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne a bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum ne, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

FCT, Abuja - Babbar Kotun Tarayya ta ci tarar jaruma Halima Abubakar N10m kan batawa fitaccen Fasto, Apostle Johnson Sulaiman suna.

Jarumar ta Nollywood ta hadu da fushin kotun ne bayan wallafa wani rubutu da ke nuna cin zarafin malamin addinin.

Kara karanta wannan

"Ka mayar da Pam matsayin shugaban NCPC": Dattawan Arewa sun buƙaci Tinubu

Jarumar fina-finai ta shiga matsala a kotu bayan bata suna ga malamin addini
Kotu ta ci tarar jarumar Nollywood, Halima Abubakar kan batawa Fasto Johnson Suleman suna. Hoto: @halimaabubakar.
Asali: Instagram

Wane mataki kotun ta dauka kan jarumar?

Kotun ta kuma dakatar da Halima daga dukkan wallafa wani abu da zai batawa malamin suna, a cewar Leadership.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Fasto Suleman ya na zargin jarumar da wallafa bayanan karya a kansa a shafinta na Instagram wanda aka wallafa a wasu jaridu.

Malamin addinin ya ce jarumar ta kira shi da munanan sunaye inda ta ce shi mai neman mata ne kuma mugu da sauran sunaye marasa dadin ji.

Damar kare kai da kotun ta ba jarumar

Yayin da ya ke yanke hukunci, alkalin kotun, Mai Shari'a, Enobie Obanor ya ce an ba Halima damar kare kanta amma ta gaza.

Obanor daga bisani ya yanke hukunci inda ya ba Fasto Suleman gaskiya tare da cin tarar jarumar, cewar rahoton Daily Post.

An ci tararta N10m kan wallafar da ta yi a shafin Instagram tare da bata umarnin da ta janye kalamanta a shafin.

Kara karanta wannan

Eid-el-Fitr: Gwamnatin tarayya ta bayyana ranaku 2 na hutun Sallah

An kama Fasto a kwara kan damfara

A baya, mun kawo muku labarin cewa Hukumar EFCC ta cafke shugaban cocin CAC Freedom City a jihar Kwara kan zargin damfara.

Faston mai suna Adeniyi Abiodun ya shiga hannu ne kan zargin damfarar mambobin cocinsa zunzurutun kudi har N3.9m.

Shugaban sashen yaɗa labarai na hukumar EFCC, Dele Oyewale shi ya tabbatar da hakan a wata sanarwa da ya fitar a ranar Asabar 6 ga watan Afrilun 2024.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.