Rikici da Malamin Addini: Dr. Idris Dutsen Tanshi Ya Dawo Bauchi Bayan Gudun Hijirar Kwanaki

Rikici da Malamin Addini: Dr. Idris Dutsen Tanshi Ya Dawo Bauchi Bayan Gudun Hijirar Kwanaki

  • Sheikh Idris Abdulaziz Dutsen Tanshi ya samu tarba daga magoya bayansa, inda suka taro shi daga bayan gari har zuwa kofar gidansa
  • Dalibansa sun ce malamin ya samu gagarumar nasara cikin wata hijira da ya yi ta tsawon makonni
  • Sun kuma bayyana yanayin da suka shiga tun bayan hijirar ta sa da kuma jin labarin dawowarsa gida

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum

A yau Litinin ne Dr. Idris Dutsen Tanshi ya dawo Bauchi bayan ya shafe makonni yana gudun hijira zuwa kasar waje.

Dr. Idris Dutsen Tanshi
Daliban malamin sunce ya samu gagarumar nasara cikin hijirar da yayi. Hoto: Dutsen Tanshi Majlis Bauchi Asali: Facebook
Asali: Facebook

A faifayin bidiyon da shafin Dutsen Tanshi Majlis Bauchi ya wallafa, Dr. Idris ya iso Bauchi ne cikin rakiyar jami'an tsaro da dandazon dalibansa.

Kara karanta wannan

Tsohon gwamna ya bayyana babbar matsalar Najeriya da Tinubu ya fara magancewa

Dr. Idris yayi hijira ne yayin da rikici ya barke tsakaninsa da gwamnatin Bauchi bayan sabani da suka samu.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Duk da cewa gwamnatin da nesanta kanta da dambarwar, Dr. Idris ya sha nanata cewa gwamnan Bauchi, Bala ne ke masa bita-da-kulli.

Daliban malamin sun magantu bayan dawowarsa

Kai tsaye bayan dawowar malamin gida aka fara gabatar da muhadara a masallacinsa da ke Bauchi.

Daliban da suka gabatar da karatun sun nuna farin cikinsu ga dawowar malamin sun kuma ce akwai gagarumar nasara da suka samu

Sun kuma tabbatar da cewa ba za su yi kasa a gwiwa ba wajen ci gaba da kira a kan tauhidi.

Sai dai har zuwa lokacin kammala wannan rahoton malamin bai gabatar da wani jawabi ba.

Dalilin yin Hijirar Dr. Idris Dutsen Tanshi

A karatukan da malamin ya gabatar kafin ya yi hijira, ya bayyana dalilai da suka tilasta masa kaura.

Kara karanta wannan

Gwamnati za ta dauki mataki bayan gano masu ɗaukar makamai, su aikawa miyagu

Daga ciki ya bayyana matsin lamba da ya samu daga gwamnati, ya kuma nuna yin hijira halas ne idan mutum ya samu kansa a irin yanayin.

Kafin Hijirar Dutsen Tanshi, meya faru?

Kafin hijirar malamin, an gurfanar da shi a gaban kotu inda aka zarge shi da neman tada hankalin al'umma.

Zargin ya kai ga kai shi ga gidan gyaran hali kafin daga baya a ba da belinsa bayan shafe wata guda.

Lauya ya fadi inda malamin yayi hijira

A tun farko, biyo bayan neman malamin da hukuma ta yi ruwa a jallo da samamen da ta kai gidansa, ya yanke shawarin yin hijira.

Sai dai tun bayan wani yunkurin cafke shi da hukuma ta yi a ranar 24 ga watan Janairu malamin ya yi batan dabo.

Lauyan ya ce malamin ya kaura ne zuwa inda zai samu kubuta daga makircin da ake kokarin shirya masa.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng