Saudiya Ta Fara Neman Watan Shawwal, Ta Fadi Lokacin Sanar da Makomar Azumi
- Hukumar kasar Saudiya ya ce ta fara duba jinjirin watan Shawwal 1445 wanda zai alamta kawo karshen watan Ramadan
- Kamar yadda rahotanni suka bayyana, masu neman watan na samun matsala a aikinsu, wanda ake fargabar ba lallai a ga watan yau ba
- Sai dai Saudiya ta ce za ta ci gaba da duba watan har zuwa karfe 6:30PM (agogon Makkah) inda za ta yanke hukuncin karshe
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida
Hukumar kasar Saudiya, ta sanar da cewa ta fara neman ganin watan Shawwal 1445 wanda zai alamta kawo karshen watan Ramadan.
A cewar shafin Inside the Haramain na Facebook, ganin watan a yau Litinin zai tabbatar da cewar gobe Talata za ayi hawan karamar Sallah.
"Har yanzu ba a ga wata ba" - Saudiya
Kamar yadda hotuna mabanbanta suka nuna yadda ake duban watan, Saudiya ta ce an fi karkatar da neman watan ne a biranen Sudair da Tumair.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Hakazalika, sanarwar Inside the Haramain ya nuna cewa Kotun Koli ta Saudiya za ta sanar da hukuncin ganin watan da misalin karfe 6:30PM (agogon Makkah).
Sai dai da alama ba za a iya ganin watan a yau Litinin baz sakamakon wahalar ganinsa da kwararrun masu duba suka bayyana.
Hukuncin da Saudiya ta yanke
Duk da hakan, kasar ta ce za ta ci gaba da duba watan har zuwa lokacin da aka kayyade a hukumance, kafin ta sanar da sakamakon karshe.
Bayan kai karfe 6:30 na yammaci ba tare da an ga watan ba, hukumar Saudiya ta yanke hukuncin cewa ranar Laraba ce za ta zama ranar Sallah.
Hasashen yanayi a ranakun Sallah
Tun da fari Legit Hausa ta ruwaito cewa hukumar kula da yanayi ta Nijeriya (NiMET) ta sanar da cewa za a yi tsananin rana a ranakun bukukuwan Sallah.
NiMET ta fitar da sanarwar cewa za a iya samun hadari da ruwa a wasu sassa na Arewa, amma mafi akasarin lokuta rana ce mai zafi.
Gwamnatin tarayya ta ayyana Talata da Laraba a matsayin ranakun hutun bikin karamar Sallah, kamar yadda ministan cikin gida ya sanar.
Asali: Legit.ng