Ramadan 2024: Dole Za a Cika Azumi 30 a Najeriya, Masana Ilimin Taurari

Ramadan 2024: Dole Za a Cika Azumi 30 a Najeriya, Masana Ilimin Taurari

  • Masana sun bayyana dalilan da za su sa dole sai 'yan Najeriya sun cika azumi 30 a wannan shekarar
  • Sun lissafo kasahe sama da 20 a fadin duniya da dole sai sun yi azumi 30, sun ce ko sun yi amfani da na'ura ba za su ga wata ba
  • Mai martaba sarkin Musulmi ya ba da muhimmiyar sanarwa yayin da ake daf da kammala azumin watan Ramadan

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Najeriya - A lokacin da azumin watan Ramadan na shekarar 2024 yake ƙoƙarin karewa, al'ummar Musulmi a fadin duniya za su fara duba jinjirin watan Shawwal ranar Litinin.

Ganin watan Shawwal ne zai tabbatar da ƙarshen azumin watan Ramadan da fara bukukuwan sallah.

Masana ilimin taurari
Masanan sun shawarci 'yan Najeriya su rika kaucewa anfani da labaran bogi akan lamarin ganin wata. Hoto: Ibrahim Shehu Giwa/ Simwal Usman Jibril
Asali: Facebook

Sai dai masana ilimin taurari sun fara nuni da cewa lalle azumin wannan shekarar sai ya cika 30 wanda hakan ke nuna cewa ko da an duba watan ranar Litinin ba za a gan shi ba.

Kara karanta wannan

Saudiya ta fara neman watan Shawwal, ta fadi lokacin sanar da makomar azumi

Simwal Usman Jibril, wani masanin ilimin taurari, ya tabbatar da cewa lalle ganin wata ba zai yiwu ba ranar Litinin, saboda haka ya shawarci 'yan Najeriya da su shirya yin azumi 30.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Yaushe jinjirin wata zai bayyana?

Malam Muhammad Salihu Yakubu, masanin ilimin ya tabbatar da cewa watan zai fito ne ranar Litinin bayan faduwar rana da minti 41 wanda hakan ba zai ba da damar ganin shi ba koda an yi anfani da na'ura.

Ya kuma kara da cewa watan watan zai fito ranar Talata ta yadda za a gan shi ya karkata kadan yana kallon Arewa.

Dalilin da ya sa ba za a ga wata ba

Masanan sun ce jinjirin watan za a haife shi ne bayan rana ta fadi ranar Litinin, wanda hakan ke nuni da cewa watan Ramadan zai cika kwana 29 da awa 9 da minti 20 da dakiku 28.

Kara karanta wannan

Bukukuwan Sallah: NiMet ta yi hasashen za ayi zafin rana da tsawa daga Litinin zuwa Laraba

Saboda haka ganin watan ba zai yiwu ba a yinin Litinin, dole sai ranar Talata 9 ga watan Afrilu.

Kasashen da ba za'a ga wata ba

Malam Yakubu ya lissafa kasashe guda 23 wanda yace dole su cika azumi 30 ciki har da tarayyar Najeriya.

A cewarsa, dukkan kasashen da suka fara azumi ranar Litinin, 10 ga watan Maris, dole sai sun cika azumi 30.

Ga jerin kasashen:

  1. Najeriya
  2. Algeria
  3. Iraqi
  4. Bahrain
  5. Burkina Faso
  6. Masa
  7. Mauritania
  8. Turkiyya
  9. Mali
  10. Falasdinu
  11. Saudi Arabia
  12. Dubai
  13. Yemen
  14. Guinea Bissau
  15. Qatar
  16. Senegal
  17. Kuwait
  18. Lebanon
  19. Sudan
  20. Syria
  21. Tunisia
  22. Ivory Coast

A guji shan ruwa a Ramadan

Masanan sun ja hankalin 'yan Najeriya akan su guji yada jita-jita a lokacin da ake sauraron sanarwar ganin wata daga fadar mai marbata Sarkin Musulmi.

Sannan sun kara da cewa dole ne kowa ya cika azuminsa domin duk wanda yayi Sallah ranar Talata to ya sha ruwa a Ramadana.

Kara karanta wannan

Mafita mafi sauki: Reno Omokri ya ba 'yan Najeriya shawarin yadda za su shawo kan karyewar Naira

Kiran mai martaba sarkin Musulm

Duk da bayanai da suke fitowa daga masana ilimin taurari, mai martaba Sarkin Musulmi yayi kira ga dukkan Musulmin Nijeriya da su fita domin duba wata a yammacin Litinin.

Ya kuma bukaci a gaggauta sanar da majalisar shi ta hanyoyin da suka dace da zarar anga jinjirin watan.

Asali: Legit.ng

Online view pixel