Majalisa Ta Tsige Mataimakin Gwamnan PDP, Bayanai Sun Fito

Majalisa Ta Tsige Mataimakin Gwamnan PDP, Bayanai Sun Fito

  • Majalisar dokokin jihar Edo ta ɗauki matakin tsige mataimakin gwamnan jihar, Philip Shaibu, daga kan muƙaminsa
  • Ƴan majalisar sun ɗauki wannan matakin ne biyo bayan gabatar da rahoton kwamitin bincike kan zarge-zargen da ake yi wa Shaibu
  • Kwamitin binciken ya samu Philip da laifi ɗaya cikin biyu da ake zarginsa da aikatawa, inda ya bada shawarar a sauke shi daga kan mulki

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

Jihar Edo - Majalisar dokokin jihar Edo, ta tsige mataimakin gwamnan jihar, Kwamared Philip Shaibu.

Majalisar ta ɗauki wannan matakin ne a kan Philip Shaibu a ranar Litinin, 8 ga watan Afirilun 2024 a yayin zamanta, cewar rahoton jaridar Leadership.

Majalisa ta tsige Philip Shaibu
Majalisar dokokin jihar Edo ta tsige Philip Shaibu Hoto: Rt. Hon. Philip Shaibu
Asali: Facebook

Tsigewar ta biyo bayan amincewa da rahoton kwamitin bincike na mutum bakwai da majalisar ta kafa domin bincikar zarge-zargen da ake yi wa Shaibu.

Kara karanta wannan

Mataimakin gwamnan da aka tsige ya mayar da martani mai zafi, ya tona wani babban sirri

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Tunda farƙo dangantaka ta yi tsami a tsakanin gwamnan jihar, Godwin Obaseki da Philip Shaibu, bayan mataimakin gwamnan ya nuna sha'awar tsayawa takarar gwamna.

Meyasa aka tsige Philip Shaibu?

A yayin zaman majalisar, shugaban masu rinjaye na majalisar, Charity Aiguobarueghian, ya bayyana rahoton kwamitin binciken, rahoton tashar Channels ya tabbatar.

Charity ya ce kwamitin ya gano abubuwa guda biyu tare da bayar da shawara guda ɗaya.

Aiguobarueghian ya ce yayin da rahoton kwamitin ya kasa tabbatar da zargin yin ƙarya aka yi wa mataimakin gwamnan, an same shi da laifin bayyana sirrin gwamnati.

A bisa haka, sai kwamitin binciken ya bada shawarar a tsige mataimakin gwamnan bisa dalilin bayyana sirrin gwamnati.

Magatakardan majalisar Yahaya Omogbai ya ƙirga ƴan majalisar da suka kaɗa ƙuri'a domin a tsige Philip Shaibu.

Mambobi 18 daga cikin 19 da suka halarci zaman majalisar sun kaɗa ƙuri'ar tsige mataimakin gwamnan yayin da ɗaya ya ƙauracewa kaɗa ƙuri'a.

Kara karanta wannan

Gwamna ya naɗa matashi ɗan shekara 37 a matsayin sabon mataimakin gwamna

Shaibu ya yi rashin nasara

A wani labarin kuma, kun ji cewa Babbar kotun tarayya mai zama a Abuja ta ƙi amincewa da buƙatar mataimakin gwamnan jihar Edo, Kwamared Phiip Shaibu.

Alƙalin kotun mai shari'a James Omotoso ya yi fatali da buƙatar Shaibu na dakatar da majalisar dokokin jihar Edo daga yunƙurin tsige shi da ta ke yi.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng