Tuhuma Kan Aikata Laifuffuka 26, Emefiele Ya Isa Kotu, Ya Gurfana Gaban Alkali
- A yanzu haka tsohon gwamnan babban bankin Najeriya (CBN), Godwin Emefiele ya isa babbar kotun Legas domin gurfana gaban alkali
- Hukumar EFCC ce ta shigar da shi kara tare da wani Henry Isioma Omoile bisa zargin aikata laifuffuka 26 da suka shafi zamba da rashawa
- Ana kuma tuhumar Emefiele da bayar da cin hanci ga abokan huldarsa da karbar na goro wanda ya sabawa dokar cin hanci ta Najeriya
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida
Legas - Tsohon gwamnan Babban Bankin Najeriya (CBN), Godwin Emefiele, ya isa babbar kotun jihar Legas da ke Ikeja yayin da za a gurfanar da shi bisa zargin cin zarafin ofis.
Jaridar Leadership ta ruwaito cewa an gurfanar da Emefiele tare da Henry Isioma Omoile a gaban kotun mai shari’a Rahman Oshodi kan sabbin tuhume-tuhume 26.
Laifuffukan da ake tuhumar Emefiele
Ana zargin mutanen biyu ne da karbar rashawa, karbar kyaututtuka ta hanyar wakilai, cin hanci da rashawa, da karbar kadarori ta hanyar zamba.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
An kuma zarge shi da bayar da cin hanci da rashawa ga abokan huldar sa wanda ya sabawa dokar cin hanci da rashawa ta shekarar 2000.
Talabijin na Channels ya rahoto lauyan hukumar da ke yaki da yi wa tattalin arziki tu’annati (EFCC), Rotimi Oyedepo (SAN) ne ya shigar da tuhumar a ranar 3 ga watan Afrilu.
Akwai shari'ar Emefiele a Abuja
Idan ba a manta ba, tuni EFCC ta gurfanar da Emefiele a babbar kotun tarayya Abuja bisa zarge-zargen karkatar da kudi a lokacin da yake gwamnan CBN.
Hukumar ta kuma zargi Emefiele da aikata laifuffuka da suka hada da:
"Ware kudaden kasashen waje a jimillar kudi na dalar Amurka 2.1bn ba tare da bin ka'ida ba, wanda hakan ya saba wa ‘yancin ‘yan Najeriya.”
Ma'aikata 40 sun rasa aiki a CBN
A wani labarin kuma, babban bankin Nijeriya (CBN) ya kori ma'aikata 40 a wani yunkuri na yin garambawul a bankin.
Legit Hausa ta ruwaito cewa mafi akasarin ma'aikatan 40 da aka kora sun fito daga sashen kudi na bankin (DFD).
An sallami akalla darakoci 22 daga sashen DFD, sai 18 daga sashen kula da lafiya, ciki har da Zgabawa Bulus, mataimakin daraktan CBN.
Asali: Legit.ng