Eid-El-Fitr: Gwamnatin Tarayya Ta Bayyana Ranaku 2 Na Hutun Sallah

Eid-El-Fitr: Gwamnatin Tarayya Ta Bayyana Ranaku 2 Na Hutun Sallah

  • Gwamnati ta ayyana ranaku 2 na Talata da Laraba su kasance ranakun hutu ga ma'aikata domin gudanar da bikin karamar Sallah
  • Ministan harkokin cikin gida, Dr. Olubunmi Tunji-Ola ya sanar da ranakun hutu a madadin gwamnatin tarayya a ranar Lahadi
  • Tuni daga Legit Hausa ta ruwaito cewa a yau Lahadi shugaban kasa Bola Tinubu ya shilla zuwa Legas inda zai yi bikin Sallah a can

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Abuja - Gwamnatin tarayya ta ayyana ranar Talata, 9 ga wata da ranar Laraba, 10 ga watan Afrilu a matsayin ranakun hutun bikin karamar Sallah.

Gwamnatin tarayya ta ayyana ranakun hutun bikin karamar Sallah
Eid-El-Fitr: Gwamnati ta zabi Talata da Laraba a matsayin ranakun hutu. Hoto: Olubunmi Tunji-Ola, Bola Ahmed Tinubu
Asali: Twitter

Ministan cikin gida, Dr. Olubunmi Tunji-Ola, ya sanar da hakan a madadin gwamnatin tarayya, kamar yadda jaridar The Guardian ta ruwaito.

Kara karanta wannan

Karin kudin wuta: Kano da sauran jihohi 12 da suka shirya inganta wuta ga al'ummarsu

A cikin wata sanarwa dauke da sa hannun sakatariyar ma'aikatar, Dr. Aishetu Gogo-Ndayako, ministan ya taya Musulmi murnar kammala azumin Ramadan.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Gwamnatin tarayya ta yi kira ga Musulmi

Tunji-Ola ya yi kira ga al'umar Musulmi da su yi riko da kyautatawa, soyayya, hakuri da zaman lafiya wanda suka koya daga Annabi Muhammad.

Jaridar Tribune ta kuma rahoto ministan ya nemi 'yan Nijeriya da su ci gaba da nuna hadin kai da kaunar junansu wanda zai wanzar da zaman lafiya a kasar baki daya.

"Ministan ya na yi wa daukacin al'umar Musulmi murnar zagayowar bikin karamar Sallah, tare da yin addu'ar samun ladar Ubangiji daga ibadar azumi da suka gudanar."

A cewar sanarwar.

Idan har an ga wata a ranar Litinin, to ana sa ran ranar Talata ta zama ranar da Musulmi za su sha ruwa, idan kuma ba a gani ba, to Laraba ce za ta zama ranar Sallah kai tsaye.

Kara karanta wannan

Bikin karamar Sallah: Tinubu zai shilla zuwa Legas, fadar shugaban kasa ta fadi lokaci

Tinubu ya tafi Legas bikin karamar Sallah

Tun da fari, Legit Hausa ta ruwaito cewa shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya shilla zuwa Legas domin gudanar da bikin Sallah.

Mai magana da yawun shugaban kasar, Ajuri Ngelale ne ya sanar da hakan a ranar Asabar, tare da yi wa al'umar Musulmi barka da Sallah.

Hakazalika, Ngelale ya kuma bayyana cewa Tinubu zai ci gaba da gudanar da ayyukansa na ofis da zarar ya kammala hutun Sallah.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i.