Dan Majalisa Ya Fadi Kokarin da Zai Yi Domin a Samu Tsaro a Jihar Zamfara
- An daɗe ana fama da matsalar rashin tsaro a jihar Zamfara wacce ta daɗe tana cin tuwo a ƙwaryar al'ummar jihar
- Ɗan majalisar da ke wakiltar Gusau/Tsafe ya shirya yin duk mai yiwuwa domin sanya gwamnatin tarayya ta tura ƙarin sojoji a jihar
- Kabiru Maipalace ya bayyana hakan ne lokacin da ya kai ziyarar jaje ga mutanen garuruwan Tsafe da Magazu kan hare-haren ƴan bindiga
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi
Jihar Zamfara - Ɗan majalisar wakilai, Honarabul Kabiru Maipalace ya ce gwamnatin tarayya za ta tura ƙarin dakarun sojoji zuwa Zamfara.
Ɗan majalisar ya bayyana hakan ne a lokacin da ya kai ziyarar jaje ga al’ummar Tsafe da Magazu da ke ƙaramar hukumar Tsafe a jihar Zamfara, cewar rahoton jaridar The Nation.
Maipalace ya kai ziyarar ne a ranar Asabar, 6 ga watan Maris kan hare-haren da ƴan bindiga da suka kai a yankin.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
A baya-bayan nan ne ƴan bindiga suka kai hari a garuruwan biyu inda suka kashe mutane da dama tare da yin garkuwa da wasu masu yawa.
Wane ƙoƙari ɗan majalisar zai yi?
Maipalace, wanda yake wakiltar mazaɓar tarayya ta Gusau/Tsafe a majalisar wakilai ya ce zai yi duk mai yiwuwa don ganin an tura ƙarin dakarun sojoji zuwa yankin, rahoton jaridar The Guardian ya tabbatar.
A kalamansa:
"Domin haka ina son ku ɗan ƙara haƙuri, za a jibge jami’an tsaro da yawa a nan domin ƙarfafa tsaron rayuka da dukiyoyi a yankin.”
A yayin ziyarar, ɗan majalisar ya gudanar da taron tattaunawa tare da mutanen garuruwan biyu.
Da yake jawabi a fadar sarkin Tsafe, ɗan majalisar ya bayyana harin a matsayin mummuna kuma abin takaici.
A kalamansa:
"Na zo nan ne domin jajantawa jama’a game da hare-haren ƴan bindiga da aka kai a garin nan."
"Abin takaici ne matuƙa yadda harin na baya-bayan nan ya kai ga kashe kwamandan rundunar tsaro ta CPG."
Jihar Zamfara ta kulle iyakokinta
A wani labarin kuma, kun ji cewa gwamnatin jihar Zamfara ta sanya dokar kulle iyakokinta da jihohin Katsina da Sokoto.
Dokar taƙaita zirga-zirgar za ta riƙa aiki ne daga ƙarfe 7:00 na yamma zuwa ƙarfe 6:00 na safe.
Asali: Legit.ng