Shugaban Miyetti Allah Ya Jefa Gwamnan APC Cikin Matsala Kan Tilasta Masa Kafa Kungiya

Shugaban Miyetti Allah Ya Jefa Gwamnan APC Cikin Matsala Kan Tilasta Masa Kafa Kungiya

  • Yayin da ake ci gaba da tsare shugaban kungiyar Miyetti Allah, Bello Badejo ya bayyana wanda ke bayan matsalar da ya shiga
  • Badejo ya ce Gwamna Abdullahi Sule ne ya umarce shi da jagorantar kungiyar da ake zargin ta ta’addanci ne a jihar Nasarawa
  • Shugaban kungiyar ya bayyana haka yayin da ake ci gaba bincike bayan kama shi kan zargin kafa kungiyar ta’addanci ba bisa ka’ida ba

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

Jihar Nasarawa – Shugaban kungiyar Miyetti Allah, Bello Badejo ya zargi Gwamna Abdullahi Sule na jihar Nasarawa kan kafa kungiyar Zaman Lafiya.

Badejo ya bayyana haka ne yayin da ake tuhumarsa inda ya ce gwamnan ne ya matsa masa ya kirkiri kungiyar.

Kara karanta wannan

Rikicin El-Rufai da Uba Sani: PDP ta gaji da lamarin, ta nemo mafita ga gwamnan Kaduna

Shugaban Miyetti Allah ya kira sunan gwamnan APC kan zarginsa da ake yi
Shugaban Miyetti Allah, Bello Badejo ya ce Gwamna Sule na Nasarawa ne ya tilasta masa kafa kungiyar da ake zarginsa. Hoto: Bello Badejo, Abdullahi Sule.
Asali: Facebook

Yaushe aka cafke shugaban Miyetti Allah?

Shugaban kungiyar wanda ake tuhuma da zargin ta’addanci an cafke shi ne a ranar 23 ga watan Janairu a karamar hukumar Karu da ke jihar.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Daga bisani an gurfanar da shi a gaban Babbar Kotun Tarayya kan tuhume-tuhume guda uku ciki har da ta’addanci.

An zargi Badejo da kirkirar kungiyar kabilar Fulani da ake kira ‘Kungiyar Zaman Lafiya’ ba tare da neman izinin hukumomi ba.

Badejo ya zargi Gwamna sule da yi masa tilas

Punch ta tattaro Badeje na fadawa masu bincikensa cewa gwamnan shi ne ya goyi bayan kirkirar kungiyar.

Ya ce ya samu kiran waya daga gwamnan inda ya ke bukatarsa da ya jagoranci kungiyar sa kai daban da sauran wadanda ake da shi.

“An kama ni ne saboda wasu ‘yan banga da na ke jagoranta a jihar Nasarawa a farkon watan Janairu.”

Kara karanta wannan

NERC ta tsokano ‘yan kwadago, ana yi wa Tinubu barazana saboda kudin lantarki

“Gwamna Sule ne ya kira ni kan Kungiyar Zaman lafiya inda na ce masa ban san da ita ba amma ya ce ya na son kirkirar kungiyar sa kai kamar yadda wasu jihohi suka yi.”
“Gwamnan ya tambayen ko zan yi aiki a Akajo wanda shi ne shugaban kungiyar, na ce masa ba zan iya aiki da Akajo ba, daga bisani na kira Akajo kan yadda za mu gudanar da kungiyar.”

- Bello Badejo

Badejo daga bisani ya fadawa Sarkin Lafia cewa mutane suna korafi kan ayyukan kungiyar shi kuma bai son haka inda ya ce suna bata sunan Gwamna, cewar Pulse.

An kama shugaban Miyetti Allah

Kun ji cewa jami’an tsaro sun cafke shugaban kungiyar Miyetti Allah kan zargin ta’addanci da ake yi kansa.

Ana zargin Bello Badejo da kirkirar kungiyar Zaman Lafiya ba tare da neman izinin hukumomi ba a jihar Nasarawa.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.