Ganduje Ya Burma Matsala Bayan Bankado Takardun Kotu Kan Badakalar Kamfanin Auduga

Ganduje Ya Burma Matsala Bayan Bankado Takardun Kotu Kan Badakalar Kamfanin Auduga

  • Yayin Gwamna Abba Kabir ya kafa kwamitin bincike kan Umar Ganduje, wasu takardu sun bankado yadda aka yi badakala
  • Takardun da aka gano daga kotun na zargin yadda Ganduje ya siyar da kamfanin auduga ga iyalansa ba bisa ka’ida ba
  • Wannan na zuwa ne bayan gwamnatin jihar ta kafa kwamtin binciken Ganduje da iyalansa kan karkatar da kadarorin gwamnati

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

Jihar Kano – Wasu takardu a kotu sun bayyana yadda tsohon gwamnan jihar Kano, Abdullahi Ganduje ya siyar da kamfanin auduga ga iyalansa.

Takardun sun zargin Ganduje da siyar da kamfanin da ke Challawa ga kamfanin Lesage wanda mallakin iyalansa ne.

Kara karanta wannan

Zargin rashawa: Ganduje ya magantu kan binciken da gwamnatin Kano za ta yi masa

Sabbin takardun kotu sun bayyana yadda Ganduje ya yi badakala a Kano
Bayanai sun bayyana yadda aka zargi Umar Ganduje da badakala a kamfanin auduga a Kano. Hoto: @OfficialAPCNg, @Kyusufabba.
Asali: Twitter

Zargin da ake kan Ganduje a kamfanin auduga

Daily Nigerian ta tabbatar da cewa takardun na dauke da zargin cewa Ganduje ya siyar da kamfanin a N320m inda aka yi ittifakin darajarsa ya kai N750m.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Takardun har ila yau, sun bayyana cewa ba a tura kudin zuwa asusun gwamnati ba yayin da aka dauke duk wasu takardu da ke da alaka da cinikin daga gwamnati.

Daga cikin takardun da ke dauke da korafe-korafe kan Ganduje akwai zargin matarsa, Hafsat Abdullahi ita kadai ke da ikon saka hannu domin fitar da kudi a kamfanin.

Har ila yau, ‘ya’yan Ganduje guda hudu sune darektocin kamfanin kuma masu hannun jari a ciki.

Daga cikin darektocin akwai Umar Asiya Abdullahi da Umar Abdul’azeez Umar da Umar Muhammad Abdullahi da kuma Zainab Abdullahi.

Sai kuma Fatima Abdullahi a matsayin sakatariyar kamfanin wadanda dukkansu ‘ya’yan tsohon gwamnan jihar ne.

Kara karanta wannan

Bayan Kaduna, Gwamnan APC ya zargi uban gidansa da yashe lalitar gwamnati gaba ɗaya

Masu gabatar da karar sun bayyana cewa a watan Satumbar 2017, Ganduje ya amince da siyar da kadarar ga iyalansa ba tare da bin ka’ida ba.

Abba Kabir ya kafa kwamitin binciken Ganduje

Wannan na zuwa ne bayan Gwamna Abba Kabir ya kafa kwamitocin shari’a kan binciken yadda aka karkatar da kadarorin gwamnati a jihar.

Gwamnan na zargin tsohon Gwamna, Umar Ganduje da siyar da kadarorin gwamnati ba tare da bin ka’ida ba daga 2015 zuwa 2023.

Abba ya gargadi masu raba tallafin abinci

Kun ji cewa Gwamna Abba Kabir na jihar Kano ya yi gargadi kan karkatar da kayan tallafi da ya kaddamar karo na hudu.

Abba ya ce ba zai taba bari wasu tsiraru su karkatar da kayan ba inda ya ce zai dauki mummunan mataki kan haka.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.