Ba A Haka: Atiku Ya Taimakawa Tinubu da Shawarwari Kan Karin Kudin Wutar Lantarki

Ba A Haka: Atiku Ya Taimakawa Tinubu da Shawarwari Kan Karin Kudin Wutar Lantarki

  • Atiku Abubakar yana ganin babu tausayi a yadda gwamnatin tarayya ta amincewa kamfanoni su kara kudin lantarki
  • ‘Dan takarar shugaban Najeriyan a 2019 da 2023 ya ce an sake jefa Bayin Allah a karin kunci bayan cire tallafin fetur da Dala
  • Atiku ya ba gwamnatin tarayya shawarwarin yadda yake ganin ya kamata a bi wajen gyara harkar wutar lantarki a Najeriya

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

M. Malumfashi ya shafe shekaru ya na kawo labaran Hausa musamman na siyasa, addini, tarihi, wasanni da al’ada.

Abuja - Tsohon mataimakin shugaban Najeriya, Atiku Abubakar ya yi tir da yadda gwamnatin Najeriya ta tashi kudin lantarki.

Babban jagoran adawan kasar bai goyon bayan karin kudin shan wutar lantarkin da aka yi wa ‘yan rukunin farko da ake kira Band A.

Atiku Abubakar, Asiwaju Bola Ahmed Tinubu
Atiku Abubakar ya soki karin kudin lantarki a Najeriya Hoto: Atiku Abubakar, Asiwaju Bola Ahmed Tinubu
Asali: Facebook

Atiku ya ce Tinubu bai da tsausayi

Kara karanta wannan

PDP: Kungiyoyi sun ambaci Minista a cikin wadanda za a ladabtar saboda cin amana

A wasu jeringiyar maganganu da ya yi a shafin X a ranar Juma’a, Atiku Abubakar ya sake sukar manufofin gwamnatin Bola Tinubu.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Atiku Abubakar ya zargi gwamnatin tarayya da kawo tsare-tsare masu zafi ba tare da ba da isasshen lokacin saukake wahalhalu ba.

‘Dan takaran shugabancin kasar a zaben 2023 ya ce an yi karin kudin lantarkin ne a lokacin da ‘yan Najeriya suke tsakiyar kunci.

Lantarki: Shawarar Atiku ga gwamnatin Tinubu

Wazirin Adamawa ya ce cire tsarin tallafin man fetur da karya darajar Naira da bankin CBN ya kawo karin wahala ga al’umma.

"Kamfanoni za su fi tasirantuwa ta mummunar hanya. Bayan yawan ruwa da suke biya a kan bashin banki, suna kashe kudi sosai a kan dizil, da albashi mai yawa a dalilin sabon tsarin albashi."

Kara karanta wannan

Gwamnati ta ce za ta kuma kara kudin wutar lantarki, ta fadi dalili

"Mutanen shugaban kasa suna jefa tattalin arziki cikin matsala mai zurfi. Babu tausayin jama’a a manufofinsa."
"Yana da muhimmanci a fahimci tushen matsalar harkar wutar lantarki kafin a fito da wasu salon gyare-gyare."
"Lokaci ya yi da za a duba saida kamfanonin lantarkin da aka yi da ya haifar da DISCOS."

- Atiku Abubakar

A bayanin da ya yi a shafin Facebook, Atiku ya ce dole a bi a hankali, a kawo tsare-tsaren da za su takaita wahalar da ake ciki.

Sannan 'dan siyasar ya ce sai NERC ta tashi tsaye, a inganta samun hasken wuta.

Ya aka tashi kudin lantarki?

A makon nan gwamnati ta sanar da karin kudin lantarki ga abokan huldar da ke sahun farko wadanda suka fi kowa samun wuta.

Wannan karin na 300% yana zuwa ne yayin da 'yan Najeriya ke fama da rashin wutar lantarki a cikin zafi kuma a watan azumi.

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng