Mahaifiyar Mataimakin Gwamna a Arewa Ta Riga Mu Gidan gaskiya, an Yi Ta'aziyya

Mahaifiyar Mataimakin Gwamna a Arewa Ta Riga Mu Gidan gaskiya, an Yi Ta'aziyya

  • Rahoto da muke samu yanzu na nuni da cewa mahaifiyar mataimakin AbdulRahman AbdulRasaq ta riga mu gidan gaskiya
  • Mama Ena Maud Alabi, mahaifiya ce ga mataimakin gwamnan Kwara, ta rasu ne a safiyar ranar Juma'ar nan
  • Tuni da gwamnan jihar Kwara, AbdulRahman AbdulRazaq da kuma Sarkin Ilorin suka mika sakon ta'aziyya

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Ilorin, jihar Kwara - Mahaifiyar mataimakin gwamnan jihar Kwara, Mama Ena Maud Alabi ta rasu.

Mahaifiyar mataimakin gwamnan jihar Kwara ta rasu
Gwamnan jihar Kwara ya mika sakon ta'aziyyar rasuwar mahaifiyar mataimakinsa. Hoto: @followKWSG
Asali: Twitter

Mama Alabi, wacce haifaffar ƙasar Jamaica ce amma ta yi aure a Najeriya ta rasu a safiyar Juma'a tana da shekaru 98.

Jaridar Leadership ta ruwaito cewa Mama Ena ta kasance malamar asibiti a asibitin mata na Amilegbe da ke Ilorin har zuwa lokacin ritayarta a shekarar 1980.

Kara karanta wannan

Ana fama da tsadar rayuwa, dan majalisar APC ya gwangwaje 'yan mazabarsa

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Gwamnan Kwara ya mika sakon ta'aziyya

A cikin wani sakon ta'aziyya a X, gwamnan jihar Kwara, AbdulRahman AbdulRazaq, ya misalta Mama Ena a matsayin mace mai son hidimtawa jama'a.

Sanarwar da aka wallafa a shafin gwamnatin jihar na Twitter, dauke da sa hannun sakataren watsa labarai na gwamnan, Rafiu Ajakaye, ta kara da cewa:

"A madadin iyalan AbdulRazaq, gwamnati da jama'ar jihar Kwara, gwamnan na mika sakon ta'aziyya ga mataimakin gwamna, iyalai da abokan arziki kan wannan rashi."

Gwamnan ya yi addu'ar Allah ya gafarta wa marigayiyar tare da ba iyalanta hakurin jure wannan babban rashi na uwa ta gari.

Sarkin Kwara ya mika sakon ta'aziyya

Haka zalika, Sarkin Ilorin, Alhaji Ibrahim Sulu-Gambari, ya mika sakon ta'aziyya ga mataimakin gwamnan jihar, Mr Kayode Alabi, bisa mutuwar mahaifiyarsa.

Sulu-Gambari wanda ya yi wa marigayiyar kyakkyawan fata, ya kuma nemi iyalan Mama Ena da su dauki hakuri na wannan rashi.

Kara karanta wannan

Kungiyar Kudu ta shiga sabgar Arewa, ta ba gwamna shawara kan Matawalle

Mallam Abdulazeez Arowona, mai magana da yawun sarkin ne ya fitar da sanarwar ta'aziyyar.

Sarkin ya jaddada cewa Mama Ena ta kasance mace da ya kamata ayi koyi da kyawawan halayenta na yi wa jama'a hidima.

Ya ba mataimakin gwamnan tabbacin cewa masarautar Ilorin tana jimami da kuma yin makoki na rashin mahaifiyarsa.

Mata 10 mafi arziki a duniya

A wani rahoton, Legit Hausa ta tattaro bayani game da kididdigar mujallar Forbes na mutanen da suka fi kowa arziki a duniya, inda a wannan shekarar mata suka karu zuwa kaso 13.3%.

Akalla mata 10 ne a yanzu taurarinsu ke haskawa a duniyar masu arziki, inda Françoise Bettencourt Meyers ke ci gaba da rike kambun mace mafi arziki a duniya.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i.