Rai bakon duniya: Babar mai martaba Sarkin Ilori ta rasu tana shekara 124

Rai bakon duniya: Babar mai martaba Sarkin Ilori ta rasu tana shekara 124

Innalillahi wa inna ilaihi raji’un, Allah Yayi ma mahaifiyar mai martaba Sarkin Ilori, Alhaji Ibrahim Sulu Gambari, Alhaja Aishat Nma Sulukarnaini rasuwa, kamar yadda kanuwar shugaban majalisar dattawa, Sanata Bukola Saraki, Sanata Gbemisola Rukayyat Saraki ta bayyana.

Legit.ng ta ruwaito Sanata Gbemisola Rukayyat Saraki ta sanar da mutuwar dattijuwar ne a shafinta na kafar sadarwar zamanita Facebook, inda tace Alhaja Sulukarnaini ta rasu ne da yammacin Litinin, 3 ga watan Yuni.

KU KARANTA: Almubazzarancin 3.4bn: Hukumar yaki da rashawa ta shawarci Ganduje ya dakatar da Sarki Sunusi II

Rai bakon duniya: Babar mai martaba Sarkin Ilori ta rasu tana shekara 124

Babar mai martaba Sarkin Ilori ta rasu tana shekara 124
Source: Facebook

Sanata Gbemisola Rukayyat Saraki ta bayyana cewa mahaifiyar Sarkin ta rasu tana da shekaru 124 a duniya, kuma jigo ce a masarautar Illori gaba da baya saboda kasancewarta

- Jika ga Sarkin Illori na 7

- Diya ga Sarkin Illori na 8

- Matar Sarkin Illori na 9

- Kanwar Sarkin Illori na 10

- Mahaifiyar Sarkin Illori na 11

Ana sa ran yi ma dattijuwar jana’iza a ranar Talata, 4 ga watan Yuni, wanda tayi daidai da ranar karamar Sallah, a fadar mai martaba Sarkin Illori dake garin Illorin jahar Kwara.

Da fatan Allah Ya jikan mahaifiyar Sarki Sulu Gambari, Alhaja Aishat Nma Sulukarnaini, Allah Yayi mata rahama, Ya kai haske kabarinta, Ya kuma baiwa iyalanta da kafatanin al’ummar masarautar Illori hakurin rashi.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Source: Legit

Mailfire view pixel