Hukumar EFCC Ta Cafke Fitaccen Ɗan Daudu a Najeriya, Bobrisky a Legas
- Hukumar EFCC a jihar Legas ta kama fitaccen dan daudu a Najeriya, Idris Okuneye a daren jiya Laraba 3 ga watan Afrilu
- Ana zargin Idris da aka fi sani da Bobrisky da watsa takardun naira da kuma keta haddin takardar naira a Legas
- Wannan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da kakakin hukumar, Dele Oyewale ya fitar da safiyar yau Alhamis
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne a bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum ne, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.
Jihar Legas - Hukumar EFCC ta cafke fitaccen ɗan daudu a Najeriya, Idris Okuneye da aka fi sani da Bobrisky.
Hukumar ta dauki matakin ne bayan zargin Bobrisky da watsa takardun naira da kuma cin mutuncinta wanda ta sabawa doka.
Bobrisky: Matakin da EFCC ke shirin dauka
Bobrisky wanda ke jawo cece-kuce a kwanakin nan an tsare shi a ofishin hukumar da ke jihar Legas.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Kakakin hukumar, Dele Oyewale shi ya tabbatar da haka a shafin hukumar na Facebook a yau Alhamis 4 ga watan Afrilu.
Oyewake ya ce an kama Bobrisky ne a daren jiya Laraba 3 ga watan Afrilu inda ya ce za a tura shi kotu da zara an kammala bincike.
Martanin hukumar EFCC kan Bobrisky
"Tabbas mun kama Bobrisky, ya na tare da mu yanzu haka a ofishinmu da ke Legas a daren jiya Laraba."
"Mun cafke shi ne kan watsa takardun Naira da kuma cin zarafin kudin wanda hakan ya sabawa dokar kasa."
"Babu batun wasa a kokarin mu na dawo da darajar Naira, duk da muna kan bincike amma za mu gurfanar da shi a gaban kotu."
- Dele Oyewale
EFCC sun fara bincike kan bashin Emefiele
A baya, mun kawo muku labarin cewa Gwamnan babban bankin Najeriya (CBN), Olayemi Cardoso ya bayyana cewa hukumomin tsaro sun fara bincike kan kuɗin ƙasashen waje.
Cardoso ya ce hukumomin tsaro ciki har da hukumar EFCC ke gudanar da bincike kan yadda aka yi da kuɗin.
Wannan na zuwa ne yayin da ake ci gaba da tuhumar tsohon gwamna CBN, Godwin Emefiele lokacin da ya ke gwamnan bankin..
Asali: Legit.ng