Ana Cikin Tsadar Rayuwa Gwamnatin Tinubu Ta Shirya Ninka Kudin Wutar Lantarki

Ana Cikin Tsadar Rayuwa Gwamnatin Tinubu Ta Shirya Ninka Kudin Wutar Lantarki

  • Gwamnatin tarayyar Najeriya ta gaji da biyan kuɗin tallafi kan wutar lantarki ga miliyoyin ƴan kasar nan
  • Cire tallafin zai sanya farashin wutar lantarki ya ƙaru da sama da kaso 300% duk da halin tsadar rayyuwar da ake ciki
  • Gwamnatin ta yi bayanin cewa ƙarin zai sanya a samu sababbin masu zuba hannun jari a ɓangaren da rage kuɗin da take kashewa

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

FCT, Abuja - Farashin wutar lantarki zai ƙaru a Najeriya bayan gwamnati ta shirya cire tallafin da take bayarwa.

Kamfanonin rarraba wutar lantarkin za su samu damar ƙara kuɗin wutar lantarkin zuwa N200 ($0.15) kan kowace sa'a ɗaya ga masu amfani da ita a birane a wannan watan, cewar rahoton Daily Trust.

Kara karanta wannan

Gwamnatin jihar Sokoto ta ciyo bashin makudan kudi? Gwamna Ahmed ya fayyace gaskiya

Gwamnatin Tinubu za ta kara kudin wutar lantarki
'Yan Najeriya za su biya kudin lantarki da tsada Hoto: Bloomberg/Contributor
Asali: Getty Images

'Yan sahun farko masu amfani da wutar a birane dai sune suka ɗauki kaso 15% na kaso 40% da gwamnati ta ce suna amfani da wutar lantarki a ƙasar nan, waɗanda kuma sune ƙarin zai shafa.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Gwamnatin Najeriya ta shirya ninka kuɗaɗen wutar dai har sau uku a cikin makonni masu zuwa. 

Gwamnatin za ta yi hakan ne dai domin jawo sababbin masu zuba hannun jari da rage kashe $2.3bn da take yi wajen bayar da tallafi.

Meyasa gwamnati za ta cire tallafin lantarki?

Jaridar The Punch ta ce mai ba shugaban ƙasa shawara kan yaɗa labarai da dabaru, Bayo Onanuga, ya bayyana cewa gwamnatin Tinubu za ta bari a yi ƙarin ne saboda kuɗin da take kashewa wajen samar da tallafi.

Ya bayyana cewa lokaci na ƙarshe da aka yi ƙarin kuɗin wutar a ƙasar nan shi ne a shekarar 2020, sannan ƙarin da za a yi yanzu zai sanya kamfanonin rarraba wutar su mayar da kuɗin da suka kashe tare da inganta zuba hannun jari.

Kara karanta wannan

'Yan bindiga sun yi garkuwa da ɗalibai da yawa a watan azumi, sun turo saƙo mai ɗaga hankali

A kalamansa:

"Duba da ɗumbin kuɗin da ake kashewa wajen bayar da tallafi, da tsadar farashin gas, kuɗin lantarkin da ake biya a yanzu ba mai ɗorewa ba ne."

Majalisa ta ɗagawa Tinubu yatsa

A wani labarin kuma, kun ji cewa Majalisar Dattawan Najeriya ta bukaci Gwamnatin Tarayya da ta janye kudirin cire tallafin wutar lantarki.

Majalisar tarayyar ta ce ganin yadda ake cikin wani hali a kasar bai kamata a bijiro da maganar cire tallafi a harkar wutar lantarki ba.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng