Akpabio Ya Yi Buda Baki da Sanatoci Musulmi, Ya Roki Hadin Kai Tsakaninsu da Kirista
- Shugaban majalisar dattawa, Godswill Akpabio ya yi kira ga sanatoci Musulmi da su rungumi Kirista a matsayin 'yan uwa
- Akpabio ya ce yin hakan ne zai ba 'yan majalisar damar yi wa ƙasa hidima kasancewar ubangiji daya ne ga kowa
- Ya kuma ba su tabbacin cewa bambancin addini ba zai raba kawunan 'yan majalisar ba tare da rokonsu a kan su rungumi juna
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida
Abuja - Shugaban majalisar dattawa Godswill Akpabio ya ba sanatoci Musulmi tabbacin cewa bambancin addini ba zai raba kawunansu ba.
Jaridar Daily Trust ta ruwaito cewa Akpabio ya ba da wannan tabbacin ne a wajen taron buda baki na azumin Ramadan da ya shirya masu.
Akpabio ya magantu kan Azumi da Easter
Akwai wasu sanatoci Kirista da suka halarci taron buda bakin, inda Akpabio ya ce bukin Easter da Kirista ke yi ya fado a cikin watan Ramadan.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Akpabio ya ce:
"Ina taya mu gaba daya murnar yin buda baki a yau kuma ina rokon Ubangiji ya ci gaba da jan kwananmu cikin kariyarsa.
"Wannan ne kusan karo na uku da bukin Easter ya hadu da azumin Ramadan, kenan, akwai isharar da ubangiji ke so ya nuna mana ta rungumar juna."
"Addini ba zai raba mu ba" - Akpabio
Jaridar The Punch ta ruwaito shugaban majalisar ya ce duk da cewa akwai mabiya addinai daban-daban a majalisar, sai dai ubangiji daya ne ke kula da su gaba daya.
Akpabio ya ce:
"Kamar yadda kuke gani, mun gayyaci wasu daga cikin abokan aikin mu Kirista domin ayi buda baki da su, saboda su ma suna bukin Easter.
"Akwai bukatar mu hade kanmu tare da yin aiki a matsayin 'yan uwan juna ba tare da mun bari addini ya raba kawunanmu ba."
Sanatoci na shirin tsige Godswill Akpabio?
A wani rahoto, Legit Hausa ta ruwaito cewa majalisar dattawa ta magantu kan rahoron da ke yawo na cewar wasu sanatoci na yunkurin tsige Godswill Akpabio.
Sanata Diket Plang, wanda ya musanta wannan rahoto, ya kuma ba ta tabbacin cewa Akpabio ya cike dukkan sharuddan da ake bukata kafin aka zabe shi shugaban majalisar.
Asali: Legit.ng