'Yan Bindiga Sun Kai Sabon Farmaki a Jami'ar Arewa, Sace Dalibai

'Yan Bindiga Sun Kai Sabon Farmaki a Jami'ar Arewa, Sace Dalibai

  • Ƴan bindiga sun tafka sabuwar ta'asa a jihar Taraba bayan sun kai farmaki a jami'ar tarayya da ke Wukari
  • Miyagun sun kai hari ne a ɗakin kwanan ɗalibai da ke wajen harabar jami'ar inda suka yi awon gaba da ƴan makarantar guda biyu
  • Jami'an tsaro a jami'ar sun tabbatar da aukuwar lamarin inda suka bayyana cewa an bi sahun masu garkuwa da mutanen

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

Jihar Taraba - Ƴan bindiga sun sace ɗalibai biyu na jami'ar tarayya ta Wukari a jihar Taraba.

Masu garkuwa da mutanen sun kai harin ne a ɗakin kwanan ɗalibai da ke wajen harabar jami'ar da misalin ƙarfe 10:30 na daren ranar Litinin, 1 ga watan Afirilun 2024, cewar rahoton jaridar Daily Trust.

Kara karanta wannan

'Yan bindiga sun yi garkuwa da ɗalibai da yawa a watan azumi, sun turo saƙo mai ɗaga hankali

'Yan bindiga sun kai hari a Taraba
'Yan bindiga sun sace dalibai a jami'ar tarayya da ke Taraba Hoto: @PoliceNG
Asali: Twitter

Rahotanni sun ce waɗanda abin ya shafa namiji ne da mace waɗanɗa ke karantar nazarin ƙananan halittu da tattalin arziƙi a jami'ar.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ɗakin kwanan ɗaliban dai da aka kai harin yana kan titin Wukari zuwa Zaki Biam, rahoton da jaridar Daily Post ya tabbatar.

Me jami'an tsaro suka ce kan lamarin?

Jami’ar hulɗa da jama’a ta ƴan sandan jami’ar, Adore Awudu, ta tabbatar da faruwar lamarin, inda ta ce an tattara jami’an tsaro da matasa sannan sun bi sahun masu garkuwa da mutanen.

Ko a baya dai shugaban jami'ar, Farfesa Jude Sammani Rabo, ya koka da cewa rashin isassun ɗakunan kwanan ɗalibai a jami’ar na jefa rayuwarsu cikin hatsari.

Da aka tuntuɓi kwamishinan ƴan sandan jihar Taraba, David lloyanomon ta wayar tarho, bai amsa kiran ba amma ya aika da saƙon kar ta kwana.

Kara karanta wannan

Ba a gama jimamin Kaduna ba 'yan bindiga sun shiga cikin jami'a tare da yin awon gaba da dalibai

A cikin saƙon ya bayyana cewa yana cikin wani taro domin haka a tura masa saƙo ne.

Sai dai, bayan an tura masa saƙon, ya bayar da amsa da cewa a yi haƙuri sai ya tabbatar da cewa ɗaliban jami'ar ne aka sace.

A kalamansa:

"Ina buƙatar tabbatar da ko ɗalibai ne, don Allah."

Ƴan bindiga sun sace ɗalibai

A wani labarin kuma, kun ji cewa wasu ƴan bindiga sun yi garkuwa da ɗalibai masu tarin yawa waɗanda har yanzun ba a tantance adadinsu ba a jihar Delta.

Ɗaliban sun faɗa hannun ƴan bindiga ne yayin da suke kan hanya a titin Gabas maso Yamma a yankin karamar hukumar Ughelli ta jihar

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng