'Yan bindiga sun kai harin rashin imani ana azumi, sun yi garkuwa da kananan yara 30 a Arewa
- Ƴan bindiga sun sake jefa mutane cikin tashin hankali yayin da suka sace kananan yara 30 a wani kauyen ƙaramar hukumar Batsari a Katsina
- Rahoto ya nuna cewa tun farko yaran sun fita gefen gari domin ɗibo itacen girki amma ƴan bindiga suka tattara suka tafi da su
- Zuwa yanzun babu wata sanarwa a hukumance daga gwamnatin Katsina, rundunar ƴan sanda da sauran hukumomin tsaro kan harin
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Jihar Katsina - Aƙalla kananan yara 30 ake tsammanin ƴan bindiga sun yi garkuwa da su a kauyen Kasai da ke ƙaramar hukumar Batsari a jihar Katsina.
Batsari na ɗaya daga cikin wasu kananan hukumomin jihar Katsina da ake fama da matsalar tsaro, inda hare-haren ƴan bindiga da sauran miyagun laifuka ke ƙaruwa kullum.
Har kawo yanzun da muke haɗa muku wannan rahoton, hukumomin tsaro ko gwamnati ba su ce komai ba dangane da sace kananan yaran.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Yadda lamarin ya faru daga zuwa ɗebo itace
Sai dai wani mazaunin yankin ya shaida wa gidan talabijin na Channels ta wayar tarho cewa, harin sace yaran ya faru ne da sanyin safiyar ranar Litinin.
Ya ce ƴan bindiga sun tattara yaran tare da yin awon gaba da su a bayan gari yayin da suka je nemo itacen da za a dafa masu abinci a gida, rahoton Leadership.
"Eh, harin ya afku ne jiya Litinin da safe. Yaran da adadinsu ya kai 30 sun tafi bayan gari a kauyen Kasai domin samo itacen wuta wanda iyayensu za su rika dafa musu abinci.
"Bisa rashin sa'a wasu ƴan bindiga suka tattara su, suka yi awon gaba da su zuwa wani wuri da babu wanda ya sani. Muna fata tare addu'ar Allah ya kawo mana zaman lafiya a jiharmu."
- Cewar mutumin.
Har kawo yanzu jami'in hulɗa da jama'a na rundunar ƴan sandan jihar Katsina, ASP Abubakar Sadiq, bai amsa saƙonnin da kafar ta aike masa ba kan sabon harin.
Ƴan bindiga sun sace ɗalibai a Delta
A wani rahoton kuma Wasu ƴan bindiga sun yi awon gaba da ɗalibai masu tulin yawa a yankin Evwreni da ke titin Gabas maso Yamma a Ughelli ta jihar Delta.
Rahoto ya nuna cewa ɗaliban na kan hanyarsu ta dawowa daga makaranta a jihar Kuros Riba lokacin da ƴan bindigan suka tare su.
Asali: Legit.ng