Bayan Kano, Jigawa da Bauchi, Wani Gwamna Ya Lale N3.34bn Domin Maniyyatan Hajji
- Yayin da ake ci gaba korafi kan karin kudin kujerar hajji, gwamantin jihar Kebbi ta daukewa maniyyan jihar wani kaso na kudin
- Gwamna Nasir Idris ya dauki nauyin biyan N1m ga kowane maniyyaci a jihar ciki har da wadanda suka riga suka biya kudinsu
- Wannan ya biyo bayan karin kudin kujera har N1.9m da hukumar alhazai ta yi a Najeriya kan dalilin tashin farashin dala
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.
Jihar Kebbi – Gwamnatin jihar Kebbi ta ware makudan kudi domin tallafawa maniyya aikin hajji a jihar.
Gwamna Nasir Idris ya ware N3.34bn ga maniyyata 3,344 da ke jihar domin rage musu karin kudin da hukumar alhazai ta yi.
Musabbabin daukar matakin tallafawa maniyyata
Gwamnan ya dauki wannan mataki ne bayan majalisar zartarwa a jihar ta yi ganawar gaggawa kan lamarin, cewar Premium Times.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
An gudanar da ganawar ce a jiya Litinin 1 ga watan Afrilu karkashin jagorancin mataimakin gwamnan jihar, Umar Abubakar-Tafida.
Kwamishinan yada labarai a jihar, Yakubu Ahmed ya fadawa ‘yan jaridu himmatuwar gwamnan jihar wurin inganta harkokin addini.
Yakubu ya ce wannan mataki na gwamnan zai taimakawa maniyyatan wurin biyan kudin da hukumar alhazai ta kara, a cewar rahoton Leadership.
“Daga cikin N1.9m da hukumar alhazai ta bukata, gwamnatin Kebbi ta ba kowane maniyyaci N1m yayin da sauran kudin maniyyaci zai cika da kansa.”
“Wannan tallafi zai shafi hatta wadanda suka kammala biyan kudin aikin hajji domin rage musu halin da ake ciki.”
- Yakubu Ahmed
Gwamnonin da suka tallafawa maniyyata
Gwamnoni da dama a Najeriya sun ba da tallafi ga maniyyatan jihohinsu wasu da kaso 50 yayin wasu suka biya dukkan cikon kudin.
Irinsu Simi Fubara, Bala Mohammed da Abba Kabir sun agaza. Duk da haka akwai gwamnonin da ba su yi wani yunkuri kan hajji ba.
Gwamna Jigawa ya tallafawa maniyyata
A baya, mun ruwaito muku cewa Gwamna Umar Namadi na jihar Jigawa ya tallafawa maniyyatan jihar ta N1m.
Gwamnan ya ce wadanda za su ci gajiyar wanna tallafi su ne wadanda suka gaza biyan cikon kudin da hukumar ta bukata.
Wannan na zuwa ne bayan hukumar alhazai ta kara kudin kujerar aikin hajji har N1.9m kan kowace kujera a kasar.
Asali: Legit.ng