Innalillahi: Miyagu Sun Kutsa Kai Har Ofis, Sun Kashe Babban Malamin Jami'ar Arewa
- Wasu tsageru sun shiga har ofis, sun kashe Dakta Kamal Abdulƙadir a jami'ar Maiduguri (UNIMAID) da ke jihar Borno
- Rahoto ya nuna cewa makasan sun buga masa guduma a kai tare da caka masa wuƙa, kana daga bisani suka sace motarsa da wasu kayayyaki
- Rundunar ƴan sanda ta bayyana cewa zuwa yanzun ta kama mutun 8 da ake zargin suna da hannu a kisan malamin jami'ar
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Maiduguri, Jihar Borno - An yi wa Dakta Kamal Abdulkadir, malami a sashen ilimin jiki da da kiwon lafiya na jami’ar Maiduguri (UNIMAID) kisan gilla a ofishinsa.
Dakta Abdulƙadir ya rasa rayuwarsa ne ranar Lahadi lokacin da maharan suka kutsa cikin ofishinsa, suka farmake shi dauke da wukaƙe da guduma.
Wasu majiyoyi masu ƙarfi sun shaidawa Zagazola Makama, masani kuma mai sharhi kan tsaro a tafkin Chadi cewa daga baya aka tsinci gawar lakcaran a cikin jini.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Majiyar ta ce:
"Maharan sun guntule hannunsa yayin da ya yi ƙoƙarin kare kansa daga sharrin su, sannan sun sa guduma sun fasa masa kai da ƙashin baya, nan take ya mutu."
Maharan sun kuma tafi da motarsa da wasu kayayyaki masu daraja yayin da hukumomi ke neman wadanda ake zargin, cewar rahoton Vanguard.
Ƴan sanda sun kama mutum 8
Rundunar ‘yan sandan jihar Borno ta bayyana cewa dakarunta sun cafke wasu mutane 8 da ake zargi da kashe Dakta Kamal, malami a jami'ar UNIMAID.
Kakakin rundunar ‘yan sandan jihar Borno, ASP Daso Kenneth, shi ne ya bayyana haka ga ‘yan jarida ranar Litinin a Maiduguri, rahoton Leadership.
Ya ce bayan samun rahoton faruwar lamarin, dakarun ƴan sanda suka kai ɗauki kuma sun samu nasarar damƙe mutum 8 da ake zargin suna da hannu a kisan.
"Rundunar ‘yan sanda ta samu rahoton kisan Dakta Kamal, an tabbatar da cewa an kashe shi ne a ofishinsa, kuma makasan sun sace motarsa.
"Ya zuwa yanzu dai mun kama mutane takwas kuma ana ci gaba da bincike domin bankado dukkan masu hannu a wannan aika-aika."
Sojojin sun kashe yan bindiga a jihohi 2
A wani rahoton kuma Sojoji sun samu nasarar kashe akalla 'yan bindiga 11 a samamen da suka kai jihar Zamfara da Katsina da ke Arewacin Najeriya.
Rahotanni sun bayyana cewa dakarun sun yi nasarar tarwatsa sansanin shugaban ƴan bindiga Hassan Yantagwaye a Zamfara.
Asali: Legit.ng