Abuja: Mummunar Gobara Ta Tashi a Gidan Shugaban Karamar Hukuma
- Rahotanni sun bayyana cewa gobara ta tashi a gidan shugaban karamar hukumar Kwali na babban birnin tarayya Abuja, Danladi Chiya
- Wani mazaunin unguwar mai suna Ishaya Moses wanda ya taimaka wajen kashe wutar ya ce janareta ne ya haddasa gobarar
- An tattaro cewa gobarar ta lalata wasu kayayyaki masu daraja a gidan irinsu sutura, kayan lantarki, wayoyin hannu da dai sauransu
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida
FCT, Abuja - Gobara ta tashi a gidan shugaban karamar hukumar Kwali na babban birnin tarayya Abuja, Danladi Chiya da ke yankin Lambata.
Daily Trust ta gano cewa gobarar da ta faru da misalin karfe 9:12 na safiyar ranar Juma’a, ta shafi dakin mai gadi da dakin kanwar matar shugaban karamar hukumar, Joy Abraham.
Me ya haddasa tashin gobarar?
Wani makwabcin gidan da gobarar ta kama mai suna Ishaya Moses wanda ya taimaka wajen kashe wutar ya ce janareta ne ya haddasa iftila'in.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Ya ce an kunna janaretan ne domin a jawo ruwa amma daya daga cikin wayoyin ya hade da dan uwansa, lamarin da ya haddasa gobarar.
Ya ce mai gadin gidan da ya ankara da gobarar, ya garzaya ya sanar da matar shugaban karamar hukumar da ke cikin dakinta tana shirin zuwa coci.
Gobarar ta yi mummunar barna
Moses ya ce:
“Kafin maƙwabta su kawo dauki tuni gobarar ta mamaye ɗakin mai gadin da kuma ɗakin da ’yar uwar matar shugaban ta ke zama.”
Musa ya ce kafin ‘yan kwana-kwana su iso wurin, gobarar ta kone wani bangare na gidan, kamar yadda ya ce shugaban karamar hukumar Chiya baya gida lokacin da lamarin ya faru.
An tattaro cewa gobarar ta lalata kayayyaki masu daraja a gidan irinsu sutura, kayan lantarki, takalma, wayoyin hannu da dai sauransu.
Gobara ta tashi a gidan karamar minista
A wani labarin kuma, Legit Hausa ta ruwaito cewa gobara ta tashi a gidan karamar ministar babban birnin tarayya, Mariya Mahmoud.
Rahotanni sun bayyana cewa gidan ministar da ke unguwar Asokoro ne ya kama da wuta, kuma ba a san musabbabin faruwar lamarin ba.
Asali: Legit.ng