Adeyanju Ya Lissafo Ministocin Tinubu 2 da Ya Kamata Ya Kora, Ya Zayyano Dalilai
- Gwamnatin Shugaba Bola Tinubu, wacce ta kusa cika shekara ɗaya, na fuskantar raɗe-raɗin yiwuwar sauke wasu ministoci
- Sai dai mai magana da yawun shugaban ƙasan ya yi watsi da wannan jita-jitar, inda ya yi nuni da cewa ko za a yi hakan sai bayan an kammala bincike
- Deji Adeyanju, ya soki yadda ministocin Tinubu ke gudanar da ayyukansu, inda ya nuna damuwarsu kan rashin cancantar wasu daga cikinsu
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi
FCT, Abuja - Kusan shekara ɗaya da mulkinsa, akwai jita-jita cewa nan ba da daɗewa ba Shugaba Bola Tinubu zai yi garambawul ga majalisar ministocinsa.
A cewar wani rahoto na baya-bayan nan, shugaban ƙasan na shirin fara ɗora ministocinsa da shugabannin hukumomi kan sikeli domin auna ayyukan da suka yi.
Sai dai mai magana da yawun shugaban ƙasan, Ajuri Ngelale, ya bayyana rahotannin yin garambawul a majalisar ministocin Tinubu a matsayin surutu ne kawai.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Ngelale ya ce yiwuwar sake fasalin majalisar ministocin Shugaba Tinubu zai jira har sai an kammala binciken da ake yi kan zamba a ma'aikatar kula da jin ƙai da rage talauci.
'Mafi yawan ministocin Tinubu ba su yi komai ba' - Adeyanju
Da yake zantawa da Legit.ng, ɗan rajin kare haƙƙin ɗan Adam kuma lauya, Deji Adeyanju ya ce minista ɗaya tilo a gwamnatin Tinubu da ya yi fice shi ne Olubunmi Tunji-Ojo, wanda ke jagorantar ma’aikatar harkokin cikin gida.
A kalamansa:
"Idan magana ake ta gaskiya, bayan ministan harkokin cikin gida wanda kowa ya shaida cewa ya yi abin a zo gani, babu wani ministan Tinubu da ya burge ni har zuwa yanzu."
Adeyanju ya yi nuni da cewa mafi yawan ministocin Tinubu ba su taɓuka abin a zo a gani ba kuma ya kamata a yi waje da su.
Waɗanne ministoci ya kamata a kora?
Deji ya ci gaba da cewa ministan makamashi, Bayo Adelabu da ministar mata, Uju Kennedy-Ohanenye, ba su taɓuka komai ba.
A kalamansa:
"Ministoci biyu da rashin cancantarsu ta bayyana ƙarara a fili su ne ministan makamashi wanda abin takaici mafi yawan ƴan Najeriya ke kira da 'ministan duhu' da takwararsa ta ma'aikatar harkokin mata."
Boyayyun halayen Tinubu
A wani labarin kuma, kun ji cewa mai magana da yawun shugaban ƙasa Bola Tinubu, Ajuri Ngelale, ya bayyana ɓoyayyun halayen shugaban ƙasan.
Nhelale ya yi nuni da cewa Tinubu mutum ne wanda yake tashi da wuri domin fara ayyukan kawo sauyi a ƙasa.
Asali: Legit.ng