Jigo a PDP Ya Ba Tinubu Shawara Kan Hanyar da Zai Bi Domin Faranta Ran 'Yan Najeriya

Jigo a PDP Ya Ba Tinubu Shawara Kan Hanyar da Zai Bi Domin Faranta Ran 'Yan Najeriya

  • An buƙaci Shugaba Bola Tinubu da ya ba da fifiko ga jin daɗin ƴan Najeriya biyo bayan taɓarɓarewar tattalin arziƙi da ake fama da shi a yanzu
  • A wata hira da aka yi da shi kwanan nan, Bode George, jigo a jam’iyyar PDP ya buƙaci Tinubu da ya yi abin da ya dace domin ƴan Najeriya su riƙa faɗin abubuwa masu kyau kan ƙasar nan
  • Bode George ya yi nuni da cewa akwai buƙatar shugaban ƙasan ya yi abin da ya dace domin tsamo ƴan Najeriya daga halin da suke ciki

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

FCT, Abuja - Bode George, jigo a jam’iyyar PDP, ya shawarci shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu da ya cika alƙawuran da ya yi wa al’ummar Najeriya.

Kara karanta wannan

Shugaba Tinubu ya fadi abin da 'yan Najeriya suka yi wanda ya cancanci yabo

Jigon na PDP yayin da yake martani kan halin da ƙasar nan ke ciki, ya ce cika alƙawuran da Tinubu ya yi zai ƙarfafa gwiwar ƴan Najeriya su riƙa faɗin kyawawan abubuwa kan ƙasar nan.

Bode George ya shawarci Tinubu
Bode George ya bukaci Tinubu ya cika alkawuran da ya dauka ga 'yan Najeriya Hoto: Chief Olabode George, Asiwaju Bola Ahmed Tinubu
Asali: Facebook

George, ya bayyana hakan ne yayin da aka yi hira da shi a shirin 'Politics Today' na gidan talabijin na Channels tv, a ranar Juma'a, 29 ga watan Maris 2024.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ya kuma yi martani kan jawabin da Shugaba Tinubu ya yi a ranar Alhamis, 28 ga watan Maris, inda ya buƙaci ƴan Najeriya da su riƙa yin addu'a da daina la'antar ƙasar nan.

Wace shawara Bode George ya ba Tinubu?

Dattijon ya ce jawabin na Shugaba Tinubu abu ne mai sosa rai amma ƴan Najeriya za su so su gani a ƙasa.

A kalamansa:

Kara karanta wannan

Jami'an Binance da aka tsare ya maka NSA da EFCC kara a gaban kotu, ya zayyano bukatunsa

"Waɗannan duk kiraye-kiraye ne kawai, abin da ya kamata ya biyo baya shi ne a samar da wata hanya wacce za ta tabbatar cewa an ba mutane fata, musamman matasan da ba su da aikin yi, ba su da madogara. Wannan shi ne abin da yake sa mutane su yi abubuwa marasa kyau
"Sannan idan aka ce akwai tsananin talauci a ƙasa, mutane za su kasance cikin fushi. Ina tausayawa mutanenmu, sannan ina son Tinubu ya yi abin da ya dace ta hanyar ba mutane fata mai yawa."

Buhari ya kira Tinubu

A wani labarin kuma, kun ji cewa Tsohon shugaban kasa, Muhammadu Buhari ya sake taya Shugaba Tinubu murnar cika shekaru 72 a duniya.

Buhari ya sake taya shi murna bayan kiran waya da ya yi masa ta musamman domin bikin ranar haihuwarsa.

Asali: Legit.ng

Online view pixel