"Na Samu Bashin $587m, N85bn", Uba Sani Ya Tona Yadda El-Rufai Ya Bar Kaduna

"Na Samu Bashin $587m, N85bn", Uba Sani Ya Tona Yadda El-Rufai Ya Bar Kaduna

  • A karon farko Uba Sani ya yi magana game da tulin bashin kudin da aka ci a Kaduna kafin ya zama gwamna
  • Gwamnan ya nuna takaicinsa a kan aron da aka karbo, an bar jihar Kaduna a cikin kangin biyan bashi da ruwa
  • Duk da halin da ya tsinci kan shi, Uba Sani ya ce har yau bai karbo aron kudi daga bankunan gida ko kasar waje ba

M. Malumfashi ya shafe shekaru ya na kawo labaran Hausa musamman na siyasa, addini, tarihi, wasanni da al’ada.

Kaduna - Gwamnan jihar Kaduna, Uba Sani ya ce gwamnatinsa ta gaji tulin bashin kudi da ayyuka daga gwamnatin Nasir El-Rufai.

Mai girma Uba Sani ya yi bayanin halin da gwamnatin Kaduna ta ke ciki, ya ce su na fama da biyan bashin kudin da aka karbo a baya.

Kara karanta wannan

Yaron El-Rufai ya maidawa Uba Sani martani masu nauyi kan batun bashin jihar Kaduna

Senator Uba Sani/Nasir El-Rufai
Gwamna Uba Sani ya koka cewa Nasir El-Rufai ya bar bashi a Kaduna Hoto: Senator Uba Sani/Nasir El-Rufai
Asali: Facebook

Uba Sani ya koka da bashin Kaduna

Daily Trust ta ce gwamnan ya shaida cewa a cikin N10bn da Kaduna ta samu a watan Maris, N7bn ya tafi ne a wajen biyan bashi.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Uba Sani ya fadi wannan ne a wajen wani taro da ya yi da al’umma a ranar Asabar, inda ya ce duk da haka bai taba karbo bashi ba.

Nawa El-Rufai ya bar wa Uba Sani?

A jawabinsa, gwamnan ya ce magabacinsa ya bar masa N3bn ne a cikin asusu, kudin da ba za su iya biyan albashin wata guda ba.

A kowane wata, gwamnatin Kaduna ta na kashe N5.2bn wajen biyan albashi bayan gwamnatin baya ta sallami dinbin ma’aikata.

"Abin haushi duk da dinbin bashin $587m, N85bn da ayyuka 115 da aka bari daga gwamnatin baya, mun dage wajen jagorantar jihar Kaduna zuwa ga cigaba mai dorewa."

Kara karanta wannan

Hajj 2024: Gwamnan PDP ya biya rabin kuɗin da aka ƙarawa mahajjatan jihar Arewa, ya faɗi dalili

"Mun yi cikakken binciken halin da muke ciki kuma mu na karkatar da akalarmu."
"Ina mai farin cikin sanar da ku cewa duk da bashin da muka gada a jihar, har yau ba mu ci bashin ko da kobo guda ba."

- Uba Sani

Ina Uba Sani ya dosa a Kaduna?

Punch ta rahoto gwamnan yana cewa zai fi ba da karfi kan tsaro, ilmi, kiwon lafiya da kuma tallafawa masu kananan kasuwanci.

Gwamnatin Sani da aka zaba a shekarar da ta gabata za ta samar da gidaje tare da bunkasa tattalin arziki da taimakawa jama’a.

Obasanjo ya yabi Gwamna Otti

Rahoto ya zo cewa soke dokar fansho ta sa tsohon Shugaban kasa Olusegun Obasanjo ya ga gwarzo a Gwamna Alex Otti na jihar Abia.

Obasanjo wanda shi ma yana karbar fansho, ya soki facakar da ake yi da kudin talakawa a jihohi alhali al'umma suna wahala.

Kara karanta wannan

Gwamnan Kano ya magantu kan naɗa ɗan Kwankwaso a matsayin kwamishina

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng