Mutum 50 aka kai asibiti bayan sunci naman saniya da maciji ya sara
- Saniya ce maciji ya ciza har ta mutu
- Sun ci naman saniyar sai suma suka kamu da cuta
- Babu alamar gubar ce ta kashe su, sai dai ko cin mushe
A can Afirka ta kudu, an sami mutum 50 da suka ci mushen saniya, bayan da maciji ya ciji san, har ya mutu yayi mushe.
Sai dai suma sun shiga uku bayan da aka garzaya asibiti dasu a kauyen Mpoza da ke gabashin kasar.
Sai dai Siswe Kupelo, shugaban asibitin yankin, ya bayyana wa manema labarai cewa, sun sami matsalar ne, bayan da suka ci saniyar, a bayan ta zama mushe, inda suka tsure da gudawa da amai da ma ciwon ciki, wanda ga dukkan alama cin mushen ne ko kuma gubar macijin ce ta kawo musu.
DUBA WANNAN: An gano an shawo kan cutar mama
A dai kimiyyance cin mushe yana da illa sosai, sai dai gubar maciji bata da illa muddin shanta kawai aka yi a ciki, saboda nau'in protein ce gubar, wadda a hanyar jini ne kawai zata iya lashani, ba a ciki ba.
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa
Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng