An Tafka Babban Rashi Bayan Fitaccen Darektan Fina-finai a Najeriya Ya Kwanta Dama

An Tafka Babban Rashi Bayan Fitaccen Darektan Fina-finai a Najeriya Ya Kwanta Dama

  • Masana'antar fina-finai ta tafka babban rashi bayan mutuwar babban darekta, Wole Oguntokun a jiya Laraba
  • Marigayin ya rasu ne ya na da shekaru 56 kamar yadda abokinsa, Kayode Peters ya tabbatar a shafin Instagram
  • Wannan mutuwa na zuwa ne bayan Nollywood ta tafka babban rashin jarumi, John Okafor da aka fi sani da Mista Ibu

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne a bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum ne, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

Jihar Legas - Babban direkta a masana'antar Nollywood, Wole Oguntokun ya riga mu gidan gaskiya.

Marigayin ya rasu ne a ranar Laraba 27 ga watan Maris ya na da shekaru 56 a duniya.

Fitaccen darektan fina-finai ya riga mu gidan gaskiya
Darektan fina-finan Nollywood, Wole Oguntokun ya rasu. Hoto: kayodepeters1.
Asali: Instagram

Babban rashin da aka yi a masana'antar

Abokinsa kuma daraktan fina-finai, Kayode Peters shi ya bayyana haka a shafin Instagram a yau Alhamis 28 fa watan Maris.

Kara karanta wannan

Ana daf da buda baki, Buhari ya tura sako ga Tinubu, ya yi masa ruwan addu'o'i

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Peters ya ce mutuwar fitaccen darektan abin takaici ne inda ya ce an tafka babban rashi.

Ya ce ƙasar Najeriya gaba daya ta tafka asara na fitacce kuma darekta mai kaifin basira a aikinsa.

Oguntokun wanda ya kammala Jami'ar Obafemi Awolowo, an haife shi a ranar 15 ga watan Yulin 1957.

Marigayin ya shafe fiye da shekaru 20 ya na ba da umarni bangaren shirya fina-finai musamman na bangaren wasan kwaikwayo a talabijin.

Fitaccen mawaki a Najeriya ya rasu

A wani labari mai kama da wannan, shahararren mawaki a Najeriya, Godwin Opara ya riga mu gidan gaskiya da shekaru 77.

Opara wanda aka fi sani da 'Kabaka' ya shafe fiye da shekaru 20 ya na wakan gargajiya wurin amfani da kayan kidan zamani.

Marigayin ‘Kabaka’ ya rasu ne a ranar Juma’a 22 ga watan Maris kamar yadda masu kula da wakokinsa suka tabbatar a shafukan sada zumunta.

Kara karanta wannan

Bassirou Faye: Abubuwa 6 da ya kamata ku sani kan sabon shugaban Senegal mai jiran gado

Shahararren jarumi Nollywood ya rasu

Kun ji cewa fitaccen jarumin fina-finan Nollywood, Amaechi Muonagor ya rasu bayan fama da jinya.

Amaechi kafin rasuwarsa ya sha fama da jinyar cutar hanta wanda ya har ya fito kafafen sadarwa neman taimakon.

Mutuwar Amaechi na zuwa ne kwanaki kadan bayan rasuwar fitaccen jarumi, John Okafor wanda aka fi sani da Mista Ibu.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.