Zargin Yi Wa Kasurgumin Dan Bindiga Dogo Gide Magani, Asibitin Sokoto Ya Magantu

Zargin Yi Wa Kasurgumin Dan Bindiga Dogo Gide Magani, Asibitin Sokoto Ya Magantu

  • Wani asibitin kwararru na kudi da ke jihar Sokoto, ya magantu kan zargin da ke yi na ya yi wa Dogo Gida magani kafin ya mutu
  • Asibitin mai suna Reliance Specialist, Sokoto, ya ce labarin kanzon kurege ake yadawa domin ba su taba jinyar wani dan bindiga a wajen ba
  • Rahotanni sun bayyana cewa an kashe shugaban 'yan bindiga Dogo Gide, sai dai akwai kokonto akan tabbacin mutuwarsa

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Sokoto - Asibitin kwararru na Reliance da ke Sokoto a ranar Laraba ya musanta cewa ya yi jinyar shugaban ‘yan bindiga Dogo Gide, wanda sojoji suka harbe shi.

Asibitin Sokoto ya nesanta kanva daga yi wa Dogo Gide magani
Asibitin Sokoto karyata zargin ya yi wa Dogo Gide magani. Hoto: Reliance Specialist Hospital, Sokoto
Asali: Facebook

Daily Trust ta ruwaito cewa a jiya kafafen soshiyal midiya ta cika da labaran cewa Dogo Gide ya mutu a wani asibiti da ke Sakkwato inda yake jinya bayan sojoji sun harbe shi.

Kara karanta wannan

An yi garkuwa da matar Gwamnan PDP bayan musayar wuta? Gaskiya ta bayyana

Ta'addancin Dogo Gide a Arewa

Ana kyautata zaton cewa Dogo Gide da rundunarsa ne suka yi garkuwa da sama da dalibai 100 da malaman makarantar FGC Yawuri, jihar Kebbi a 2021.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

A watan Agusta, 2023, Gide, wanda aka bayyana asalin sunansa da Abdullahi Abubakar, ya dauki alhakin harbo wani jirgin sojoji a jihar Neja.

A jiya Laraba, wasu kafofin watsa labarai suka ruwaito cewa Gide ya mutu sakamakon harbin harsashin bindiga a wata arangama da dakarun soji na OPHD makonni biyu da suka gabata.

Ba mu yi wa Dogo Gide magani ba - Asibiti

Sai dai mahukuntan asibitin Reliance Specialist da ke Sokoto sun nesanta kansu daga zargin da ake yi na cewa sun yi kokarin yi wa ɗan bindigar magani.

A cikin wata sanarwa, asibitin ya ce:

"An ankarar da mu game da jita-jitar da ake yadawa na cewa mun yi wa wani shugaban ƴan bindiga, Dogo Gide magani, kuma a asibitin mu ya mutu.

Kara karanta wannan

Akwai hannun na kusa da Buhari: Omokri ya fallasa wadanda suka kubutar da wakilin Binance

"Wannan karya ce tsagoronta, asibitinmu bai taba yi wa wani dan ta'adda musamman 'yan bindiga magani ba."

Kafofin watsa labarai irin su TVC News, da kananun jaridu irin su Daily Post da kuma Sahara Reporters sun ruwaito cewa sojoji sun kashe Dogo Gide.

Akwai ayar tambaya a mutuwar Dogo Gide

Sai dai an ruwaito cewa akwai ayar tambaya a labarin mutuwar Dogo Gide, kasancewar har yanzu babu wasu muhimman bayanai da za su tabbatar da hakan.

Wata majiya ta shaida cewa:

"Babu wata alama da muka gani daga yankin Dansadau da ke Zamfara, da za ta nuna Gide ya mutu.
"Batu kan cewa an dauko shi daga Shiroro ta jihar Neja domin yi masa magani a Sokoto ba gaskiya ba ne."

Ko da aka tuntubi kakakin rundunar 'yan sandan Sokoto, ASP Ahmad Rufa'i, ya ce shi ma ya karanta labarin mutuwar Dogo Gide ne a soshiyal midiya.

Kara karanta wannan

Jerin manyan jami'an tsaro da bincike 5 da aka taɓa tuhuma kan saɓa doka

Labarin mutuwar Dogo Gide na farko

Ba tun yau aka saba cewa an kashe shugaban 'yan bindiga Dogo Gide ba, idan ba a manta ba, a shekarar 2021, Legit Hausa ta ruwaito makamancin wannan labarin.

A lokacin an rahoto cewa mataimakin Dogo Gide, mai suna Sani Dan Makama ne ya kashe shugaban 'yan bindigar domin daukar fansar kashe Buharin Daji.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i.