Kotu Ta Yi Hukunci Kan Shari'ar Mutum 313 da Ake Zargi da Aikata Ta'addanci
- Babbar kotun tarayya da ke zamanta a birnin Maiduguri ta wanke mutum 313 da ake zargi da laifin aikata ta'addanci
- Kotun ta umurci a saki mutanen waɗanda sojoji suka cafke saboda rashin gabatar da ƙwaƙƙwarar hujja kan zargin da ake musu
- Daraktan yaɗa labarai na hukumar tsaro ya tabbatar da hakan inda ya ƙara da cewa za a miƙa mutanen hannun gwamnatin jihar Borno
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi
FCT, Abuja - Wata babbar kotun tarayya da ke jihar Borno ta bayar da umurnin sakin mutane aƙalla 313 da ake zargin ƴan ta’adda ne.
Mutanen dai sojoji ne suka cafko su bisa zargin aikata ta'addanci a lokacin da ayyukan ƴan ta'addan Boko Haram suka yi ƙamari a jihar Borno.
Meyasa kotu ta ce a sake su?
Kotun ta bayar da umarnin sakinsu ne saboda rashin samun ƙwaƙƙwarar shaidar da za ta tabbatar da zargin da ake yi musu bayan an kammala bincike, cewar rahoton jaridar The Punch.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Daraktan yaɗa labarai na hukumar tsaro, Manjo-Janar Buba Edward ne ya bayyana hakan yayin taron manema labarai a ranar Alhamis, 28 ga watan Maris a birnin tarayya Abuja, rahoton jaridar Sahara Reporters ya tabbatar.
A kalamansa:
"Kotu ta bayar da umarnin a sake su ne saboda rashin samun shaida bayan kammala bincike.
"A bisa haka, za a miƙa su zuwa hannun gwamnatin jihar Borno domin ɗaukar mataki na gaba."
Jihar Borno dai ta kwashe shekaru da dama tana fuskantar matsalar ayyukan ƴan ta'addan Boko Haram, wanda ya salwantar da rayukan mutane da dama.
Miliyoyin mutane sun rasa matsugunansu sakamakon rikicin inda suka koma ƴan gudun hijira a wasu sassan jihar da ƙasashen da ke makwabtaka da Najeriya.
Ƴan ta'adda sun miƙa wuya
A wani labarin kuma, kun ji cewa wasu kwamandojin ƴan ta'adda mutum biyu sun miƙa wuya ga dakarun sojoji a jihar Borno.
Kwamandojin ƴan ta'addan na ɓangaren Bakoura Badouma na ƙungiyar Boko Haram sun miƙa wuya ne bayan sojoji sun matsa musu da hare-hare.
Asali: Legit.ng