An Garkame Shugaban Kungiyar ’Yan Kwadago, Ana Zargin Ya Karkatar da Kayan Tallafi
- Shugaban kungiyar 'yan kwadago na jihar Yobe ya sake shiga cikin wani sabon rikici bayan da aka zarge shi da karkatar da kayan tallafi
- Kotu a Damaturu, babban birnin jihar Yobe, ta tura Kwamared Muktar Tarbutu gidan yari ne a ranar Laraba 27 ga watan Maris
- Sakataren NBA reshen jihar Yobe, Barr. Mohammad Ngumurumi, ya tabbatar da hakan, duk da cewa Tarbutu ya musanta zargin
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida
Damaturu, jihar Yobe - A ranar Laraba, 27 ga watan Maris, kotu ta garkame shugaban kungiyar kwadago ta NLC reshen jihar Yobe, Kwamared Muktar Tarbutu.
Laifin da shugaban NLC ya aikata
Kamar yadda Daily Trust ta ruwaito, an gurfanar da Kwamared Tarbutu a ranar Laraba a gaban kotun majistare II Damaturu bisa zargin karkatar da kayan tallafi.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Hukumar raya yankin arewa maso gabas (NEDC) ce jaridar Independent ta ruwaito ta ba NLC kayan tallafin domin rabawa kungiyoyi a jihar.
Sakataren kungiyar lauyoyin Najeriya (NBA) reshen jihar Yobe, Barista Mohammad Ngumurumi, ya bayyana cewa Kwamared Tarbutu bai raba kayan ba.
Ya kara da cewa Kwamared Tarbutu "bai raba wadannan kayan ga NUJ da NBA ba kuma an gurfanar da shi a yau (Laraba), amma ya ki amsa laifinsa."
Kayan tallafin da NEDC ta bayar
Lauyan ya yi bayani game da tallafin, yana mai cewa:
‘’Hukumar NEDC ta raba buhunan shinkafa 150, buhunan sukari 150, katan 150 na taliya, atamba 150 ga mata, da shaddoji 150 ga maza da kuma barguna 150.
"Bai raba wadannan kayan ga kungiyar NUJ da NBA ba, sai muka tambaye shi ina namu yake, bai nuna mana ba, shi ya sa NBA ta shigar da karar, amma da aka gurfanar da shi a yau Laraba, yaki ya amsa laifinsa."
Ngumurumi ya ce alkaliyar kotun majistare II Damaturu, Hasiya Abubakar ta aika Tarbutu gidan yari har zuwa ranar 18 ga Afrilu 2024 don sauraron karar.
"Mu ba ƴan siyasa bane" - Kungiyar ƙwadago
A wani labarin, Legit Hausa ta ruwaito cewa kungiyar ƙwadago ta TUC, ta yi wa shugaban kasa Bola Tinubu martanin cewa kungiyar ba ta da alaka da siyasa.
Shugaban kungiyar, Festus Osifo, ya ce kalaman Tinubu kan kungiyar cin fuskan ne, domin mambobinta ba yan siyasa bane amma suna da ikon yin zanga-zanga.
Asali: Legit.ng