Ramadan: Gwamna Radda Ya Faranta Ran Ma'aikatan Jihar Katsina
- Gwamnan jihar Katsina, Malam Dikko Umaru Radda ya waiwayo kan ma'aikatan jihar yayin da ake tunkarar bikin Sallah
- Gwamna Radda ya amince a biya ma'aikatan N15,000 domin su rage ɗawainiya a cikin watan Ramadan da shirye-shiryen Sallah
- Wannan kyautar kuɗin dai ta shafi dukkanin ma'aikatan jihar da ke aiki a matakan jiha da ƙananan hukumomi
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi
Jihar Katsina - Gwamnan Jihar Katsina, Malam Dikko Umaru Radda, ya amince da bada kyautar N15,000 ga ma'aikatan jihar domin azumin watan Ramadan da bikn Sallah.
Wannan kyautar kuɗin dai ta shafi dukkanin ma'aikata a matakan jiha da na ƙananan hukumomi a faɗin jihar.
Hakan na ƙunshe ne a cikin wata sanarwa da babban mataimaki na musamman ga Gwamna Radda, kan kafafen sadarwa na zamani, Isah Miqdad, ya sanya a shafinsa na X.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Ma'aikatan da za su samu kyautar kuɗin
A cewar sanarwar, gwamnan ya umurci ma'aikatar kuɗi da ta biya kowane ma'aikaci da ke aiki a matakin jiha N15,000.
Haka kuma ya umurci ma'aikatar ƙananan hukumomi da harkokin masarautu da ta biya N15,000 ga dukkanin ma'aikatan da ke aiki a matakin ƙaramar hukuma a ƙananan hukumomi 34 na jihar.
Bugu da ƙari, gwamnan ya kuma umurci ma'aikatar ƙananan hukumomin da ta biya N15,000 ga ma'aikatan da ake aiki a ƙarƙashin hukumar ilmin bai ɗaya ta SUBEB a faɗin ƙananan hukumomin jihar.
Wani ɓangare na sanarwar na cewa:
"Wannan karamcin na nuna ƙarara jajircewar da gwamna ya yi wajen kyautata rayuwar ma’aikata a Jihar Katsina.
"Matakin da gwamnan ya ɗauka na bayar da tallafin azumin Ramadan da Sallah ya nuna yadda ya jajirce wajen kyautata rayuwar ma'aikatan jihar Katsina."
Ma'aikata sun yaba
Legit Hausa ta samu jin ta bakin wani malamin makaranta a jihar mai suna Shafi'u Halliru, wanda ya yaba da wannan goron Sallah da gwamnan zai raba musu.
Ya bayyana cewa hakan abin a yaba ne kuma zai ƙara sauƙaƙawa ma'aikata sosai duba da halin da ake ciki.
A kalamamsa:
"Eh wannan abin arziƙi ne kuma an taimaki talaka, tun da an riga an yi albashi kuma har ya ƙare. N15,000 tana da daraja sosai kuma za ta taimaki mutane."
Gwamna Radda ya bada tallafi
A wani labarin kuma, kun ji cewa gwamnan Katsina, Dikko Umar Radɗa, ya raba tallafin N470m ga mutanen da hare-haren ƴan bindiga ya shafa da waɗanda annobar cutar korona ta karya.
Gwamna Raɗda ya bayyana cewa mata 550 da hare-haren ƴan bindiga ya shafa sun samu tallafin N150,000 kowanensu, jimillar kuɗin shi ne N82.5m.
Asali: Legit.ng