CBN da EFCC Sun Fara Bincike Kan Bashin da Aka Gada Daga Wajen Godwin Emefiele

CBN da EFCC Sun Fara Bincike Kan Bashin da Aka Gada Daga Wajen Godwin Emefiele

  • Babban bankin Najeriya (CBN) ya fara gudanar da bincike kan basussukan $7bn na kuɗaɗen ƙasashen waje
  • Basussukan dai an gaje su ne daga wajen tsohon gwamnan bankin na CBN, Godwin Emefiele wanda yanzu haka yake fuskantar shari'a
  • Olayemi Cardoso ya yi nuni da cewa a cikin basussukan an gano cewa $2.4bn daga cikin cikin kuɗaɗen akwai alamar tambaya a kansu

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

FCT, Abuja - Gwamnan babban bankin Najeriya (CBN), Olayemi Cardoso, ya bayyana cewa an fara bincike kan kuɗaɗen ƙasashen waje da aka ware a baya.

Cardoso ya ce hukumomin tsaro ciki har da hukumar yaƙi da yi wa tattalin arziƙin ƙasa zagon ƙasa (EFCC), ke gudanar da bincike kan yadda aka yi da kuɗaɗen, cewar rahoton jaridar The Punch.

Kara karanta wannan

Tsohon hadimin Buhari ya fadi yadda gwamnatin Tinubu za ta yi nasara

CBN na binciken bashin $2.4
CBN ya fara binciken bashin $2.4 da Emefiele ya bari Hoto: @cenbank, @OfficialEFCC
Asali: Twitter

Hakan na zuwa biyo bayan kammala tantance basussukan $7bn da bankin CBN ƙarƙashin jagorancin Cardoso ya gada daga tsohuwar gwamnatin Godwin Emefiele.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Wa CBN ya ɗauko domin binciken?

Cardoso ya ɗauko wani kamfanin bincike mai suna Deloitte, domin gudanar da bincike kan basussukan na $7bn.

A baya gwamnan na CBN ya ce kusan $2.4bn daga cikin bashin na $7bn, ba su da inganci.

Jaridar TheCable ta ce Cardoso bayan kammala taron kwamitin kula da harkokin kuɗi karo na 294 ranar Talata a Abuja, ya ce hukumomin tsaro na gudanar da bincike kan kuɗaɗen bayan rahoton na Deloitte ya nuna rashin ingancinsu.

Babban bankin, a cewarsa, yana bayar da takardun da suka dace domin taimakawa binciken.

EFCC za ta gayyato shugabannin bankuna

Cardoso ya ce hukumomin tsaron sun mayar da hankali ne wajen warware batutuwan da suka shafi hada-hadar kuɗaɗen waje da ba su cika ƙa'idoji ba.

Kara karanta wannan

Tsadar iskar gas: Jigon APC ya bukaci Shugaba Tinubu ya tausayawa talaka

Ya jaddada cewa rahoton na Deloitte ya nuna cewa yawancin hada-hadar kuɗaɗen ba su cika ƙa'idojin da za a biya su ba.

Wannan binciken dai zai sanya hukumar EFCC ta gayyato shugabannin bankuna domin su zo su bayar da bayanai.

Bankin CBN ya karya farashin dala

A wani labarin kuma, kun ji cewa babban bankin Najeriya (CBN) ya sake karya farashin dala inda aka fara siyar da ita ga ƴan canji kan farashi mai rahusa.

CBN ya sanar da ƴan canjin cewa ya siyar wa kowane ɗaya daga cikinsu $10,000 kan farashin N1,251/$.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng