Ana Daf da Gudanar da Zabe, Mai Neman Takarar Gwamnan APC Ya Riga Mu Gidan Gaskiya
- Ana tsaka da shirye-shiryen gudanar da zaben fitar da gwani, mai neman takarar gwamnan APC, Paul Akintelure a Ondo ya rasu
- Marigayin ya rasu ne da safiyar yau Talata 26 ga watan Maris yayin da ake daf da gudanar da zaben jihar a wannan shekara
- Wannan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da kakakin jam'iyyar APC a jihar, Oladapo Akintelure ya fitar da safiyar yau
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.
Jihar Ondo - Mai neman tikitin zama gwamnan jihar Ondo a zaben 2024, Dakta Paul Akintelure ya riga mu gidan gaskiya.
Akintelure wanda yana harin takara a jam'iyyar APC a zaben da za a gudanar ya rasu ne a yau Talata 26 ga watan Maris.
Yaushe marigayin ya rasu a Ondo?
Kakakin jam'iyyar APC a jihar, Alex Kalejaye shi ya tabbatar da haka ga gidan talabijin na Channels da safiyar yau Talata 26 ga watan Maris.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Marigayin wanda likita ne da ya dawo dan siyasa, a baya, ya yi korafin yadda ake masa barazana da rayuwarsa ta bangarori da dama, cewar Vanguard.
Daktan ya tsaya takarar mataimakin gwamna a zaben 2012 a jam'iyyar ACN da marigayi tsohon gwamna Rotimi Akeredolu.
Jarumin fina-finan Nollywood ya rasu
Fitaccen jarumin fina-finan Nollywood, Amaechi Muonagor ya kwanta dama ya na da shekaru 62 a duniya.
Rahotanni da aka yada a kafofin sadarwa sun tabbatar da mutuwar fitaccen jarumin a ranar Lahadi 24 ga watan Maris a jihar Anambra.
Wannan na zuwa ne kwanaki kadan bayan rasuwar wani jarumin mai suna John Okafor da aka fi sani da Mista Ibu bayan fama da jinya.
Mawaki a Najeriya ya rasu
A baya, mun ruwaito cewa wani shahararren mawaki a Najeriya, Godwin Opara ya riga mu gidan gaskiya.
Marigayin da aka fi sani da 'Kabaka' ya rasu ne bayan fama da jinya ya na da shekaru 77 a duniya.
Kabaka ya shafe shekaru fiye da 20 ya na waka da suka hada da na gargajiya wurin yin amfani da kayan kisan zamani.
Asali: Legit.ng