Halin da Najeriya Ke Ciki Ya Sa Tinubu Ya Hakura da Bikin Murnar Zagayowar Ranar Haihuwarsa

Halin da Najeriya Ke Ciki Ya Sa Tinubu Ya Hakura da Bikin Murnar Zagayowar Ranar Haihuwarsa

  • Shugaban ƙasa, Bola Ahmed Tinubu, ya yanke shawarar ƙin yin bikin cikarsa shekara 72 a duniya, sakamakon ƙalubalen da Najeriya ke fuskanta
  • Tinubu, wanda zai cika shekara 72 a ranar Juma’a, 29 ga watan Maris, ya buƙaci abokanansa da kada su shirya wani biki dominsa
  • A maimakon haka ya buƙace su da su yi amfani da kuɗaɗen wajen bayar da su ga ƙungiyoyi masu gudanar da ayyukan agaji

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

FCT, Abuja - Shugaban ƙasa Bola Tinubu ya soke gudanar da bikin murnar cika shekara 72 a duniya.

Hakan na ƙunshe ne a cikin wata sanarwa a shafin X da Bayo Onanuga, mai baiwa Tinubu shawara kan harkokin yaɗa labarai da dabaru ya fitar a yammacin ranar Lahadi, 24 ga watan Maris, 2024.

Kara karanta wannan

Tinubu ya yi magana kan ceto daliban da aka sace a Kaduna, ya sha sabon alwashi

Tinubu ya soke bikin cikarsa shekara 72
Shugaba Tinubu ya hakura da bikin murnar cikarsa shekara 72 a duniya Hoto: @OfficialABAT
Asali: Twitter

Meyasa Tinubu ya ɗauki matakin?

Shugaba Tinubu ya ɗauki wannan matakin ne saboda halin da ƙasar nan ta tsinci kanta a ciki a halin yanzu.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Shugaban ƙasan ya bada shawarar cewa kada a sanya saƙonnin fatan alheri domin zagayowar ranar haihuwarsa a gidajen rediyo da talabijin.

Shugaba Tinubu zai cika shekara 72 a duniya a ranar Juma’a 29 ga watan Maris 2024.

Wani ɓangare na sanarwar na cewa:

"Saboda halin da ƙasar nan ke ciki a yanzu da kashe jami’an soji da ƴan sandan mu a jihar Delta a baya-bayan nan da yawaitar matsalar rashin tsaro a sassan Najeriya, babu wani bikin murnar zagayowar ranar haihuwa da sanya saƙonnin fatan alheri a jaridu.
"Shugaba Tinubu ya buƙaci abokai da abokan arziƙi da ke son sanya saƙonnin fatan alherin a jaridu da su bada gudunmawar kuɗaɗen ga ƙungiyoyin agaji da suke so a madadinsa.

Kara karanta wannan

Shugaba Tinubu ya amince a kafa kasar Biyafara? Gaskiya ta bayyana

"Duk da shugaban ƙasan ya yaba da ƙwazon jami'an tsaro wajen kuɓutar da yaranmu da aka sace a Kuriga, jihar Kaduna da na jihar Sokoto, zai yi amfani da ranar haihuwarsa wajen tunani da sake sadaukar da kansa kan aikin gina ingantacciyar Najeriya."

Shugaba Tinubu ya roƙi ƴan Najeriya

A wani labarin kuma, kun ji cewa gwamnatin tarayya ƙarƙashin jagoracin Shugaba Bola Tinubu, ta buƙaci ƴan Najeria da su inganta darajar naira da kansu ba tare da saka hannun gwamnati ba.

Gwamnatin ta ce hanyar da ƴan ƙasar nan za su bi domin ɗaga darajar naira ita ce siyan kayayyaki waɗanda aka yi su a da aka yu a Najeriya.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng