Gwamna Abba Ya Karyata Masu Jita-Jita Cewa Ya Ware N6bn Don Ciyar da Kanawa a Ramadana
- Gwamnan Kano ya bayyana gaskiyar kudin da ya ware don ciyar da al'ummar jihar a cikin watan Ramadana
- Ya shawarci 'yan jarida da su daina yada labaran da basu tabbatar ba, inda ya bayyana bacin ransa kan hakan
- An fara rabon abincin buda-baki a Kano, gwamna bai ji dadi ba bayan ganin kalan abincin da ake girkawa
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Salisu Ibrahim ne babban editan sashen Hausa na Legit. Kwararren marubucin fasaha, harkar kudi da al'amuran yau da kullum ne, yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru takwas
Jihar Kano - Gwamnan jihar Kano Abba Yusuf ya musanta rahotannin da aka yada cewa gwamnatinsa ta ware Naira biliyan 6 don ciyar da mutane a watan Ramadana.
Gwamnan ya bayyana wannan batu ne a cikin wata sanarwa da ya fitar a shafinsa na X ranar Lahadi 24 ga watan Maris.
Idan baku manta ba, ganin yawan kudin da aka ce Abba ya ware ya sa APC ta fara zargin lauje cikin nadi a harkar ciyarwar.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Abba ya fadi kudin da ake kashewa
Sai dai, da yake ba da bahasi kan lamarin, Abba ya rubuta cewa:
“A ‘yan kwanakin da suka gabata, na lura da yadda kafafen yada labarai ke ta yada jita-jita game da gwamnatinmu wai mun kasafta Naira biliyan 6 don ciyar da mutane a watan Ramadan.
"Ina so in bayyana karara cewa ainihin kudin da ake kashewa a shirin shine jimillar Naira biliyan daya da miliyan dari da casa’in da bakwai da dubu dari bakwai, na tsawon wata guda.
"Ina kuma shawartar 'yan jarida da su tabbatar da cewa sun samu alkalumansu daidai game da ayyukanmu daga majiyoyin da suka dace don gujewa yada alkaluman bogi."
Abba ya fusata bayan ganin abincin da ake rabawa
Gwamnan, a ranar Juma’a, ya bayyana bacin ransa game da yadda shirin ciyarwar ke tafiya a jihar ta Kano da ke Arewa maso Yamma.
Ya bayyana rashin jin dadinsa ne a lokacin da ya kai ziyarar bazata a inda ake rabon abincin da ke Gidan Maza, a Kano ta Tsakiya.
Abba ya soki masu kula da shirin kan yadda aka jirkita yanayin abincin da kuma raba shi ga wadanda ba su aka niyyar rabawa ba.
Asali: Legit.ng