Dangote Ya Kaddamar da Rabon Buhunan Shinkafa a Kano, Sauran Jihohi Za Su Amfana
- Aliko Dangote ya ƙaddamar da shirin bayar da tallafin shinkafa ga mabuƙata a faɗin Najeriya domin rage raɗaɗi
- Attajirin wanda ya fi kowa kuɗi a nahiyar Afirika ya fara da jihar Kano inda za a raba buhunan shinkafa guda 120,000
- Shirin wanda za a yi shi a faɗin ƙananan hukumomi 774 na ƙasar nan, zai lashe kuɗi har naira biliyan 15
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi
Jihar Kano - Shugaban rukunin kamfanonin Dangote, Alhaji Aliko Dangote ya ƙaddamar da rabon buhunan shinkafa miliyan ɗaya a faɗin Najeriya.
Dangote ya fara rabon ne da buhunan farko guda 120,000 a jihar Kano, cewar rahoton jaridar Leadership.
Rabon kayan abincin wanda za a kashe Naira biliyan 15, an fara shi ne a ranar Asabar, 23 ga watan Maris, a Kano saboda yawanta.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Me yasa Dangote ya raba shinkafar?
Da yake gabatar da jawabinsa a wajen ƙaddamar da shirin, Dangote ya bayyana cewa za a raba kayan ne domin rage raɗaɗin ƙalubalen tattalin arziƙin da ake fama da shi a ƙasar nan, rahoton jaridar Premium Times ya tabbatar.
A kalamansa:
"Mun zo Kano domin mu ƙaddamar da raba buhunan shinkafa masu nauyin kilogiram 10 sama da miliyan ɗaya ga marasa ƙarfi a ƙananan hukumomi 774 na ƙasar nan kan kuɗi N15bn.
"Kason da aka ware wanda za a ba jihar Kano sabada yawan jama'a da masu fama da talauci, za mu bayar da buhuna 120,000.
"Za mu fara wannan aikin alherin ne a jihar Kano da Legas a yau, duba da bukatar samar da kayan tallafi ga masu buƙata."
Da yake karɓan kayayyakin a madadin jihar, Gwamna Abba Kabir Yusuf, ya yabawa Dangote sannan ya yi kiraga masu hannu da shuni a jihar da su yi koyi da shi.
Dangote ya sha yabo
Legit Hausa ta tuntuɓi wani mazaunin birnin Kano, mai suna Ibrahim Zulkiful, wanda ya nuna jin daɗinsa kan wannan aikin alherin da Dangote ya yi.
Ya yabawa attajiran bisa rabon shinkafan inda ya bayyana hakan a matsayin abin da ya dace kuma a lokacin da ya dace.
Ya yi fatan cewa sauran masu hannu da shuni za su yi koyi da attajirin domin taimakawa mabuƙata a jihar.
Arziƙin Dangote ya ƙaru
A wani labarin kuma, kun ji cewa attajirin da ya fi kowa kuɗi a nahiyar Afirika, Aliko Dangote, ya samu ƙarin arziƙi.
Arziƙinsa ya ƙaru da dala miliyan 141 a cikin sa’o’i 24 zuwa dala biliyan 14.8 a ranar 5 ga watan Maris na shekarar 2024.
Asali: Legit.ng