Ramadan: Gwamna Abba Ya Kai Ziyarar Bazata Waje Raba Abinci, Ya Yi Mamakin Abin da Ya Gani
- Gwamnan jihar Kano Alhaji Abba Kabir Yusuf ya bayyana rashin jin daɗinsa game da abincin da ake rabawa a azumin watan Ramadan
- Gwamna Abba ya soki rashin ingancin abincin, rashin yawansa da rashin tsafta a wajen dafa shi
- Hakan dai ya auku ne a wata ziyarar bazata da ya kai a ɗaya daga cikin wuraren da ake raba abinci da ke Gidan Maza a ƙaramar hukumar Kano Municipal
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi
Gidan Maza, jihar Kano - Gwamnan jihar Kano, Alhaji Abba Kabir Yusuf ya nuna rashin jin daɗinsa dangane da shirin ciyarwa na watan Ramadan a birnin Kano.
Gwamnan ya bayyana hakan ne a wata sanarwa a shafinsa na X a ranar Juma’a, 22 ga watan Maris 2024.
Gwamnan ya bayyana rashin jin daɗinsa da shirin a lokacin da ya kai ziyarar bazata a ɗaya daga cikin wuraren raba abincin a Gidan Maza na ƙaramar hukumar Municipal.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Gwamna Yusuf ya kuma nuna rashin gamsuwa da halin da masu gudanar da shirin ke nunawa, waɗanda yake ganin suna hana waɗanda ya kamata su ci moriyar shirin amfana da shi.
Wane umurni Gwamna Abba Kabir ya bada?
A kalamansa:
“A yammacin yau, na ziyarci Gidan Maza, ɗaya daga cikin wuraren raba abincin Ramadan a ƙaramar hukumar Kano Municipal.
"Abin da na gani a yayin ziyarar bazatan abin baƙin ciki da takaici ne, duk da isassun kayan abincin da aka ba kowane wuri.
"Tuni na bayar da umurnin gudanar da cikakken bincike, kuma na buƙaci a gudanar da canji cikin gaggawa kan wajen gudanar da shirin."
Dangote zai ciyar da mabuƙata a Kano
A wani labarin kuma, kun ji cewa gidauniyar Alhaji Aliko Dangote ta na ciyar da marasa karfi akalla 10,000 kullum a jihar Kano.
Gidauniyar ta kuma raba buhunan shinkafa miliyan daya wanda kudinsu ya kai N13bn a dukkan jihohi 36 da birnin Abuja.
Gidauniyar dai ta ɗauki wannan matakin ne domin rage raɗaɗin halin wahala da ake ciki a faɗin ƙasar nan.
Asali: Legit.ng