Yan Bindiga Sun Kashe Sabon Ango a Harin Kasuwar Arewa, an Samu Karin Bayani
- Rahotanni sun bayyana ƴan bindiga sun kashe wani sabon ango mai suna Sani a harin da suka kai kauyen Madaka da je jihar Neja.
- An ruwaito cewa makonni uku da daura wa Sani aure wannan abu ya faru a kansa, lokacin da ya je kasuwar domin yin sana'ar sayar da nama
- Haka zalika an gano yadda ƴan bindigar suka harbi ƙananan yara tare da tilasta mata karya azuminsu ko su kashe su nan take
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida
Jihar Neja - Wani sabon ango mai suna Sani yana daga cikin mutane 21 da ‘yan bindiga suka kashe a wata kasuwar mako a garin Madaka, karamar hukumar Rafi ta jihar Neja ranar Alhamis.
An kai hari Madaka a ranar Alhamis
Sani, wanda mahauci ne da ke zaune a Kagara, hedikwatar karamar hukumar Rafi, an ce ya je kasuwa ne domin sayar da nama lokacin da aka harbe shi.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Rahotan jaridar Daily Trust ya nuna cewa makonni uka da suka gabata ne aka daura aurensa.
Mazauna yankin sun ce an kaddamar da harin ne da misalin karfe 3 na yammacin ranar Alhamis lokacin da harkokin kasuwanci suka kankama.
"An tilasta mata karya azumi" - Abdullahi
Haka kuma, an ba da rahoton cewa, a yayin farmakin, 'yan bindigar sun tilasta wa mata musulmi karya azuminsu a kasuwar.
Wani mazaunin yankin mai suna Salihu Abdullahi ya shaida wa Daily Trust cewa ‘yan bindiga sun umarci matan da su karya azuminsu ko su rasa ransu.
“Muna a wani kauye da ke makwabtaka da mu inda muka je wurin hako zinare sai muka ga mutane suna gudu. Don haka, na garzaya gida a kan babur dina don kai wa iyalina dauki.
“Diyata karama na cikin wadanda suka harba, duka shekarunta 8. A tashin farko na kirga gawarwaki 11, amma daga baya an gano wasu, yayin da har yanzu ba a ga wasu ba."
- A cewar Abdullahi.
Sarkin Hausawan Madaka ya rasu
Shugaban matasan Madaka, Saidu Bwale, ya yi zargin cewa harin 'yan bindigar na ranar Alhamis na daya daga cikin mafi muni da aka kai wa al’ummar.
Sarkin Hausawan Madaka, Alhaji Garba Mai-Haja, wanda ya samu munanan raunukan harbin bindiga ya rasu a safiyar Juma’a a asibitin kwararru na IBB da ke Minna.
Mazauna yankin sun ce mutane bakwai; maza hudu da mata uku da suka hada da kananan yara suna karbar magani a asibitin kwararru na IBB.
Fada ya kaure a Neja saboda mace
A wani labarin kuma, Legit Hausa ta ruwaito cewa rikici ya kaure tsakanin kauyen Gbangba Dzuko da kauyen Tswako Makun saboda wata mace.
An ruwaito cewa wani matashi daga kauyen Dzuko ne ya yi kokarin sumbatar wata budurwa ana tsaka da gudanar da shagalin bikinta a kauyen Makun.
Asali: Legit.ng