Yan bindiga sun kaddamar da hari a jahar Neja, sun halaka mutane 8
Wasu gungun miyagu yan bindiga sun kaddamar da wata sabuwar farmaki a kauyen Kaure dake cikin mazabar Kwaki na karamar hukumar Shiroro a jahar Neja, inda suka kashe mutane 8 nan take.
Jaridar Daily Trust ta ruwaito kansilan mazabar Kwaki, Malam Jafaru Kwaki ya tabbatar da harin, inda yace da misalin karfe 8 na safiyar Lahadi, 22 ga watan Disamba ne yan bindigan suka shiga kauyen a kan babura suna ta harbe harbe.
KU KARANTA: Innalillahi wa Innailaihi raji’un: Sarkin Yakin Kazaure, Baba Santali ya rasu
“Na samu labarin sabon harin da yan bindiga suka kaddamar a garinmu, rahotanni sun tabbatar min da cewa yan bindigan suna sanye da bakaken kaya ne. sun shiga kauyen ne a kan babura suna harbin mai kan uwa da wabi.
“Daga labarin da nake samu, sun bindige mutane 8 har lahira a harin da suka kai inda suka kwashe tsawon sa’o’i suna cin karensu babu babbaka a kauyen. Har yanzu bamu san adadin mutanen da suka jikkata ba saboda mutane da dama sun tsere zuwa cikin daji dauke da raunin harsashi, amma dai mun garzaya da mutane 15 zuwa asibiti.” Inji shi.
Kansila Jafaru ya kara da cewa baya ga kashe mutane tare da jikkata wasu, yan bindigan sun yi awon gaba da shanu da dama, sun kwace ma jama’a kudade, haka zalika sun kona motoci 2, babura 5 da wasu gidaje.
A wani labari kuma, kimanin makonni uku da suka gabata ne yan bindiga suka kaddamar da wani hari a kauyen Kukoki dake cikin karamar hukumar Shiroro inda suka kashe mutane 13, tare da fatattakar mutane da dama daga kauyukansu.
Baya ga mutanen da suka kashe, su ma yan bindigan sun yi awon gaba da dakacin kauyen Madaka, Alhaji Yau Zakari, matarsa, sakataren masarautar, wani tsohon soja da kuma mutane hudu.
Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa
ko a http://twitter.com/legitnghausa
KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki
Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com
Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa
Asali: Legit.ng