Zargin Cushe a Kasafi: Tinubu Ya Dira Kan Sanata Ningi, Ya Kwance Masa Zani a Kasuwa
- Yayin da ake cece-kuce kan zargin cushe a kasafin kudi, Shugaba Bola Tinubu ya soki masu zargin an yi almundahana
- Tinubu ya ce duk wadanda ke zargin akwai matsala a kasafin kudin ya tabbata ba su da ilimi a bangaren lissafi
- Shugaban ya fadi haka ne yayin da yake shan ruwa da mambobin Majalisar Dattawa a fadarsa da ke Abuja
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.
FCT, Abuja – Shugaban kasa, Bola Tinubu ya caccaki Sanata Abdul Ningi kan zargin cushe a kasafin kudin shekarar 2024.
Tinubu ya ce duk wadanda ke zargin cushen ya tabbata ba su fahimci ilimin lissafi ba kwata-kwata.
Wane alkawari Tinubu ya yi ga Majalisar?
Shugaban ya bayyana haka a jiya Alhamis 21 ga watan Maris yayin shan ruwa da mambobin Majalisar Dattawa, a cewar Daily Trust.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Ya ce gwamnatinsa za ta yi duk mai yiwuwa domin tabbatar da hadin kai tsakaninta da Majalisar.
Ya kuma godewa Majalisar kan irin goyon baya da suke ba shi tun bayan karbar ransuwa a Majalisar.
Har ila yau, shugaban ya ce zai ci gaba da kare martabar Majalisar domin ganin an samu abin da ake so a kasar, cewar Daily Post.
Tinubu ya caccaki Abdul Ningi
“Na san lissafin da ke cikin kasafin kudin da kuma yawan lambobin da suke cikin kasafin wanda na kawo Majalisa.”
“Kuma na san lambobin da suka dawo, nagode da irin yadda kuka tafiyar da shi da kuma gudanar da kasafin.”
“Duk wadanda ke korafin akwai cushe a cikin kasafin kudin ba su fahimci ilimin lissafi ba kuma ba su yi duba zuwa ga abin da na kawo ba.”
- Bola Tinubu
Wannan na zuwa ne bayan Sanata Abdul Ningi daga jihar Bauchi ya zargi cushen N3.7trn a kasafin kudin.
Kaura ya goyi bayan Abdul Ningi
Kun ji cewa Gwamna Bala Mohammed na jihar Bauchi ya bayyana goyon bayansa ga Sanata Abdul Ningi.
Bala ya ce gwamnatinsa na tare da sanatan inda ya ce su na goyon bayansa musamman idan abin da ya ke fada gaskiya ne.
Hakan ya biyo bayan zargin cushe da sanatan ya yi a kasafin kudi wanda ya jawo aka dakatar da shi na watanni uku.
Asali: Legit.ng