Dalibai Sun Mutu a Wani Turmutsitsi a Wurin Rabon Tallafin Shinkafa a Jami'ar Arewa

Dalibai Sun Mutu a Wani Turmutsitsi a Wurin Rabon Tallafin Shinkafa a Jami'ar Arewa

  • Ɗalibai da dama sun mutu a wurin da gwamnatin jihar Nasarawa ta shirya rabon tallafin abinci ga ɗaliban jami'ar jihar
  • Rahoto ya nuna cewa tun da asubahin ranar Jumu'a, ɗaliban suka mamaye wurin da aka shirya rabon, suka kutsa cikin rumbun ajiyar da tsiya
  • Shugaban ƙungiyar ɗaliban jihar Nasarawa ya tabbatar da faruwar lamarin, inda ya ce tuni aka garzaya da waɗanda abin ya shafa zuwa asibiti

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Jihar Nasarawa - Rahotanni sun nuna akalla dalibai mata biyu na Jami’ar jihar Nasarawa sun rasa rayukansu a wani turmutsutsi a babban ɗakin taron jami’ar da safiyar Juma’a.

Wani shaidan gani da ido ya ce daliban da suka rasu na daga cikin wadanda suka yi tururuwar zuwa wurin rabon domin su samu tallafin, kamar yadda Daily Trust ta rahoto.

Kara karanta wannan

Gwamnan Arewa ya ɗauki mataki mai tsauri kan mutuwar ɗaliban jami'a a wurin wawar shinkafa

Jami'ar jihar Nasarawa.
An rasa rayuwa a wurin rabon tallafi ga ɗaliban jami'ar Nasarawa Hoto: Nasarawa State University, Keffi
Asali: UGC
"Labarin da muka samu shi ne ɗalibai mata biyu sun mutu. An ce an matse su saboda cunkoson jama'a a wurin kuka daga bisani likitoci suka tabbatar da sun mutu," in ji wata majiya

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Kamar yadda jaridar Vanguard ta tattaro, lamarin ya faru ne lokacin da ɗaliban suka je wurin da gwamnatin jihar ta shirya rabon tallafin shinkafa ga ɗaliban.

An ce daliban sun kutsa cikin ma’ajin da aka ajiye kayan abincin da za a raba da safiyar Juma’a, suka ci ƙarfin jami’an tsaron makarantar da aka jibge a wurin.

Me ya kawo turmutsitsin?

Shugaban ƙungiyar ɗaliban jihar Nasarawa ta ƙasa, Yunusa Yusuf Baduku, ya tabbatar da lamarin, yana mai cewa mafi akasarin waɗanda ibtila'in ya shafa suna asibiti.

“A zahirin gaskiya abin da ya faru a safiyar yau a Jami’ar Jihar Nasarawa da ke Keffi, abu ne mara daɗi kuma abin tausayi ne. Bayan mun gama shirin raba tallafin kwatsam ɗalibai suka zo, suka ci ƙarfin jami'an tsaro.

Kara karanta wannan

Gwamnatin Malam Dikko da sojoji sun samu gagarumar nasara kan ƴan bindiga a watan Azumi

"Sun kutsa kai ta ƙofar shiga babban ɗakin taron jami'ar inda aka ajiye buhunan shinkafar da za a raba. Abin takaicin yawancin dalibanmu mata sun sami rauni yayin da wasu suka sha wuya saboda yawan jama'a a wurin.
"A yanzu haka ina Cibiyar Kiwon Lafiya ta Tarayya da ke Keffi, inda muka kawo wasu daga cikin dalibanmu domin neman agajin gaggawa."

- Yunusa Yusuf Baduku.

Ya kara da cewa a matsayin shugaban NASA, ya samu labarin ɗaliba ɗaya ta mutu amma ba zai tabbatar da adadin waɗanda suka ji raunuka ba.

Tun kafin fara rabon lamarin ya faru

Wani ɗalibi, Abdul Yusuf ya labartawa wakilin Legit Hausa yadda aka fara wawar abincin tun kafin fara rabon yadda aka tsara.

Ya ce:

"Mata biyu ne suka mutu, abin da ya faru tun farko shi ne, shugabanni sun tsara rabon yadda za a gama lafiya, to da ɗaliban suka zo sai suka gaza haƙuri, suka sa wawa.

Kara karanta wannan

Abin da Bola Tinubu ya faɗawa sanatoci a wurin buɗa bakin azumin watan Ramadan a Villa

"Yayin haka ne aka matse wasu ɗliban, yanzu haka dai mata biyu sun mutu, wasu kuma suna kwance a asibiti, muna fatan Allah ya kawo mana karshen yunwa a ƙasar nan."

An kashe ɗan bindiga a Sokoto

A wani rahoton kuma Sojoji sun kashe wani ɗan bindiga mai hatsari da ke sanya kakin ƴan sanda yana yaudarar mutane a jihar Sakkwato.

Mai magana da yawun rundunar sojojin ƙasa, Manjo Janar Onyema Nwachukwu, ya ce sojojin sun samu wannan nasara ne ranar Laraba

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262