'Yan Bindiga Sun Tare Motar Gwamnati a Watan Azumi, Sun Tafka Ɓarna a Jihar Katsina
- Ƴan bindiga sun tare motar bas mai ɗaukar fasinjoji 18 mallakin hukumar sufuri ta jihar Katsina, sun yi garkuwa da mutane da yawa
- Ganau sun bayyana cewa maharan sun tare motar ne a yankin ƙaramar hukumar Kankara ranar Alhamis, 2 ga watan Maris, 2024
- Jihar Katsina na ɗaya daga cikin jihohin shiyyar Arewa maso Yammacin Najeriya da ke fama da ayyukan ta'addancin ƴan bindiga
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Jihar Katsina - Miyagun ƴan bindiga sun farmaki motar gwamnati da tsakar rana a yankin ƙaramar hukumar Ƙankara da ke jihar Katsina.
Rahotanni sun nuna cewa maharan sun yi awon gaba da fasinjojin motar bas mai kujeru 18 mallakin hukumar sufuri ta jihar Katsina (KTSTA).
Lamarin dai ya faru ne ranar Alhamis yayin da maharan suka tare motar bas ɗin mai lambar rijista 14B-300-KT cike da fasinjoji a hanyarsu ta zuwa Katsina.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Wani ganau ya shaida wa gidan talabijin na Channels ta wayar tarho cewa galibin fasinjojin da ke cikin motar sun fito ne daga karamar hukumar Funtua, suna hanyar zuwa Katsina.
Yadda lamarin ya faru
Waɗanda lamarin ya afku a kan idonsu sun bayyana cewa maharan sun kwashe fasinjojin motar ne a tsakanin kauyen Burdugau da ƙauyen Ƴargoje kafin su ƙarisa garin Ƙanƙara.
Har zuwa lokacin haɗa muku wannan rahoton babu wata sanarwa a hukumance daga rundunar ƴan sanda ko kuma gwamnatin jihar Katsina.
Kankara na ɗaya daga cikin kananan hukumomin mazaɓar sanatan Katsina ta Kudu da ke sahun gaba a fama da hare-haren ta'addancin ƴan bindiga.
Baya ga mazauna yankin da ke rayuwa cikin fargaba da tsoron harin ƴan bindiga, hatta matafiya da ke wucewa a kai a kai suna fargabar bin hanyar Kankara.
Gwamna Radda ya ɗauki matakai
Gwamna Dikko Umaru Raɗɗa na jihar Katsina ya ɗauki matakai tun bayan rantsar da shi domin kawo karshen ayyukan ƴan bindiga a jihar, rahoton News Direct.
Daga cikin yunƙurin da gwamnan ya yi har da kafa rundunar ƴan sa0kai waɗanda ke zakulo ƴan bindiga da masu kai masu labari da nufin warware matsalar tsaro daga tushe.
Sojoji sun halaka ɗan ta'adda
A wani rahoton kuma sojoji sun kashe wani ɗan bindiga mai hatsari da ke sanya kakin ƴan sanda yana yaudarar mutane a jihar Sakkwato.
Mai magana da yawun rundunar sojojin ƙasa, Manjo Janar Onyema Nwachukwu, ya ce sojojin sun samu wannan nasara ne ranar Laraba.
Asali: Legit.ng