Gaskiya Ta Bayyana Kan Ikirarin Bankin CBN Na Biyan Kuɗaɗen FX da Suka Maƙale a Najeriya
- Saɓanin ikirarin CBN, kamfanonin jiragen sama na kasashen waje sun musanta cewa an biya su kuɗaɗensu da suka maƙale
- Babban bankin Najeriya (CBN), a wata sanarwa, ya bayyana cewa ya biya waɗannan kuɗaɗe na kamfanonin da suka makale a Najeriya
- Amma shugaban ƙungiyar AFARN, Kingsley Nwokeoma, ya ce har yanzun bai ga wani sauyi a bashin da suke bin Najeriya ba
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Kamfanonin jiragen sama na kasashen wajen sun musanta ikirarin da babban bankin Najeriya (CBN) ya yi cewa ya warware duk wasu haƙƙokin kuɗaɗen musanya (FX).
A cewar kamfanonin har kawo yanzu babu abin da ya sauya a kuɗaɗen da suka maƙale a Najeeiya saɓanin ikirarin CBN na warware su gaɓa ɗaya.
Shugaban ƙungiyar kamfanonin jiragen sama na kasashen waje a Najeriya (AFARN), Kingsley Nwokeoma, ne ya faɗi haka yayin hira da jaridar Bussiness Day.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Ya bayyana cewa a iya abin da ya sani, babu abin da ya sauya game da kuɗaɗen kamfanonin jiragen sama da suka maƙale.
“Idan sun ce sun biya kudaden da suka makale, ya kamata su nuna mana adadinsu, su fada mana nawa ne suka biya. A karon ƙarshe da na duba, babu abin da ya sauya." in ji shi.
Shugabar AFARN ya yi zargin cewa sama da dala miliyan 700 na kuɗin tikitin su har yanzu suna makale a Najeriya, kamar yadda Leadership ta ruwaito.
CBN ya biya kamfanonin haƙƙinsu?
Tun farko muƙaddashiyyar daraktar yaɗa labarai na CBN, Hakama Sidi Ali, ta ce ba a jima ba bankin ya kammala biyan dala biliyan 7 domin biyan kuɗin da suka maƙale.
A cewata, hakan zai sa a biya a haƙƙokin musanyar kuɗaɗen waje da suka maƙale.
Bankole Bernard, shugaban kwamitin hadin gwiwar kamfanonin jiragen sama da na fasinjoji (APJC) na kungiyar zirga-zirgar jiragen sama ta kasa da kasa (IATA) ya shaidawa jaridar cewa ikirarin CBN gaskiya ne.
Ya kara da cewa an biya dukkan hakkokin kamfanonin jiragen sama da suka maƙale ma'ana babu sauran masu bin Najeriya bashin waɗannan kuɗi.
A cewarsa, an bai wa kamfanonin kasashen waje zabin karɓan kudadensu daga bankuna ta hanyar amfani da farashin I & E amma sun ki saboda suna ganin za su yi asara.
EFCC ta mayar da martani ga tsohon AGF
A wani rahoton kuma Hukumar EFCC ta ƙaryata zargin da tsohon Akanta Janar na tarayya, Ahmed Idris ya yi na cewa an hada baki da shi don kullawa wani sharri.
Jami'in hukumar, Mahmud Tukur, ya shaidawa kotun tarayya da ke Abuja cewa, hukumar ba ta da wani nufi na kulla wa tsohuwar ministar kuɗi sharri.
Asali: Legit.ng