An Kama Mutumin da Ya Yi Barazanar Kashe Shugaban EFCC Na Ƙasa, Ya Faɗi Gaskiya

An Kama Mutumin da Ya Yi Barazanar Kashe Shugaban EFCC Na Ƙasa, Ya Faɗi Gaskiya

  • Dakarun EFCC sun cafke mutumin da ya yi barazanar kashe shugaban hukumar, Ola Olukoyede bayan ya bankaɗo sirrin watan ƙungiyar addini
  • A watan Janairu, 2024, shugaban EFCC ya bayyana cewa sun gano wata ƙungiyar addini da ke safarar makudan kuɗi ga ƴan ta'adda a Najeriya
  • Wannan labarin ne ya jefa wanda ake zargi, Kayode Cole, cikin matsala lokacin da ya yi barazanar cewa shugaban EFCC zai mutu nan da watanni 6

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

FCT Abuja - Jami'an hukumar yaƙi da masu yi wa tattalin arziƙi zagon ƙasa (EFCC) sun damke mutumin da ya yi ɓarazanar kashe shugabanta, Ola Olukoyede.

Jami'an sun damƙe mutumin mai suna, Kayode Cole, kan ikirarin da ya yi a dandalin sada zumunta cewa nan da wasu ƴan watanni shugaban EFCC zai bar duniya.

Kara karanta wannan

Kisan sojoji a Delta: Daga karshe an fadi dalilin da ya sa aka kashe jami'an tsaron

Shugaban EFCC, Ola Olukoyede.
EFCC ta kama wanda ya yi barazanar kashe shugaban hukumar Hoto: OfficialEFCC
Asali: Twitter

Hakan na kunshe ne a wata sanarwa da hukumar EFCC ta wallafa a shafinta na manhajar X wanda aka fi sani da Twitter a ranar Laraba.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Mai magana da yawun hukumar EFCC, Dele Oyewale, ya ce sun yi nasarar kama Mista Cole a yankin Lugbe da ke babban birnin tarayya Abuja.

Wace barazana mutumin ya yi?

Cole dai ya yi barazanar kisan ta shafinsa na Instagram “1billionsecretss," yayin da yake tsokaci kan labarin da fitaccen shafin nan, Instablog9ja, ya wallafa ranar 1 ga watan Fabrairu.

Shafin ya buga labari mai taken, "ƙungiyar addini na safarar kuɗi zuwa ƴan ta'adda: Mun gano N7bn da aka tura zuwa ga wata ƙungiyar addini - shugaban EFCC."

Da yake mayar da martani a sashen sharhi na Instablog9ja, Cole ya ce shugaban EFCC zai mutu nan da watanni shida masu zuwa.

Kara karanta wannan

Kotu ta yanke hukunci kan mutumin da ya sace Alkur'anai a Masallaci, ta ba shi zaɓi 1 a Abuja

“Zai mutu nan da wata shida. Mutumin nan zai mutu nan da watanni 6, zaku ce ni na fada maku,”

- inji shi.

A yayin da ake yi masa tambayoyi, wanda ake zargin ya yi iƙirarin cewa ya bi zuga ne kawai, amma ba wai da gaske yake yi ba.

Ta'addanci: EFCC ta gano kungiyar addini

Idan ba ku manta ba, a ranar 30 ga watan Janairu, 2024, shugaban EFCC ya bayyana cewa sun bankado yadda wata ƙungiyar addini ke safarar kuɗaɗe ga ƴan ta'adda.

Ya ce EFCC ta kuma ci karo da wata ƙungiyar addinin da ke kokarin kare kuɗaɗen da aka yi safararsu bayan an bi diddigin kuɗin har zuwa asusun ƙungiyar.

Tinubu ya jero masu yaƙarsa

A wani rahoton na daban Bola Ahmed Tinubu ya ce masu amfana da tallafin man fetur da ƴan fasa kwauri ba su haƙura ba, sun koma suna yaƙar gwamnati

Yayin ganawa da shugabannin APC na jihohi, Tinubu ya jaddada cewa gwamnatinsa na aiki ba dare ba rana domin inganta rayuwar jama'a

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262