Ramadan: Magidanci Ya Bayyana Yadda Yake Tafiya Mai Nisa Don Samun Abincin Buda Baki Ga Iyalansa

Ramadan: Magidanci Ya Bayyana Yadda Yake Tafiya Mai Nisa Don Samun Abincin Buda Baki Ga Iyalansa

  • Al'ummar musulmi a faɗin duniya na ci gaba da gudanar da azumin watan Ramadan na shekarar 1445AH
  • Wani magidanci a jihar Gombe ya yi bayyana yadda yake tafiyar kilomita 9.5 domin zuwa karɓo abincin buɗa baki na sadaka
  • Ya yi nuni da cewa yana da ƴaƴa tara waɗanda yake samu yana ciyarwa idan ya samu sadakar abincin da ake rabawa

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

Jihar Gombe - Wani magidanci mai suna, Amadu Galadima, mai shekaru 49 a duniya, ya bayyana tsawon lokacin da yake kwashewa domin zuwa karɓar abincin buɗa baki na azumin Ramadan.

Magidancin mai ƴaƴa tara na daga cikin waɗanda suka ci gajiyar shirin ciyarwa na watan Ramadan na bana da wata ƙungiyar agaji ta ‘Charity Association Margarity’ ta ƙasar Bulgaria ta shirya a ƙaramar hukumar Dukku ta jihar Gombe.

Kara karanta wannan

Gwamnatin Tinubu ta fallasa sunayen masu daukar nauyin ta'addanci, za ta dauki mataki

Abincin buda baki na Ramadan
Kungiyar na raba abincin buda baki ga mabukata Hoto: Haruna Musa Dukku
Asali: Facebook

Jaridar Daily Trust ta ce Amadu ya gaya mata cewa yana yin tafiyar kilomita 9.5 a kullum daga ƙauyensu zuwa Dukku domin samun abincin buɗa baki ga iyalansa.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Wace hanya magidancin ke samo abincin?

Ya bayyana cewa a wasu lokutan ya kan samu masu babura su rage masa hanya.

A kalamansa:

"Wasu bayin Allah masu zuwa Dukku a babur su kan rage min hanya ta yadda zan iya zuwa inda ake raba abincin. Abincin da ake rabawa yana da kyau sosai.
"A wajen dawowa, wasu lokutan sai na yi tafiya mai nisa kafin na haɗu da wanda zai rage min hanya zuwa gida.
"Idan na samu abincin, ina kaiwa iyalaina sannan da ƙyar na ke ɗan tsakura nasa a bakina.
Ina da yara tara, biyar mata huɗu maza, wannan abincin yana taimaka mana sosai domin ba mu da abin da za mu ci a gida."

Kara karanta wannan

Murna yayin da Shugaba Tinubu ya fadi lokacin da tsadar rayuwa za ta kare a Najeriya

Jagoran ƙungiyar a Najeriya, Alhaji Hafiz Muhammad Sulaiman, ya ce a kullum suna ciyar da aƙalla mutum 300, da suka haɗa da zawarawa, marayu, almajirai da sauran marasa galihu.

Ramadan: Ɗan takara ya bada tallafi

A wani labarin kuma, kun ji cewa tsohon ɗan takarar gwamnan PDP a jihar Gombe, Abdulkadir Hamma Saleh ya ba shugabanin jam'iyyar a jihar goron azumi.

Hamma Saleh ya ba manyan jam'iyyar PDP a jihar tallafin N7.8m domin su yi azumin watan Ramadan cikin walwala.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng