Sabon Tsarin da Gwamnati ta Kawo Ya Jawowa Dangote da Kamfanoni 6 Tafka Asarar N1.7tr a 2023
- A shekarar 2023 darajar kuɗin Najeriya ta yi raga-raga bayan gwamnati ta fito da tsarin da naira za ta nemo haƙiƙanin darajarta da kanta
- Hakan dai ya jawo manyan kamfanoni sun yi asarar maƙudan kuɗaɗe wajen yin canjin kuɗaɗen ƙasashen waje
- Kamfanin Dangote, MTN da wasu manyankamfanoni biyar sun sanar da yin asarar N1.7tr a shekarar da ta gabata
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi
FCT, Abuja - Dangote, Nestle da MTN tare da wasu kamfanoni huɗu na Najeriya sun tafka asarar N1.7tr saboda faɗuwar darajar naira a shekarar 2023.
Jaridar The Punch ta ce kamfanonin dai sun yi wannan asarar ne a shekarar 2023 saboda matsalolin da suka shafi canjin kuɗaɗen ƙasashen waje.
Wasu kamfanoni suka yi asarar N1.7tr?
Rukunin kamfanonin Dangote a cikin bayanan kuɗaɗensa na shekarar 2023, ya yi asarar N164bn.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Kamfanin ya ce wannan asarar dai ta samu ne galibi saboda ayyukan da yake yi a wasu ƙasashen.
- BUA
Kamfanin BUA, shi ma ya yi asarar N69.9bn. Hakan ya nuna ƙari mai yawa kan asarar da kamfanin ya yi a shekarar 2022 ta N5.5bn.
- Nigerian Breweries
Kamfanin Nigerian Breweries, a cikin rahoton bayanan kuɗaɗensa na shekarar 2023, ya yi asarar N153bn, saɓanin asarar N26.3bn da ya yi a shekarar 2022.
- Nestle
Asarar ta kuma shafi kamfanin Nestle Nigeria. Kamfanin ya ce saboda faɗuwar darajar naira, ya yi asarar N195.bn, a cewar rahoton jaridar Daily Trust.
- MTN
A ɓangaren sadarwa, kamfanin MTN ya yi asarar kuɗaɗen da suka kai N740.4bn.
Hakan na nufin an samu ƙarin kaso 804% idan aka kwatanta da asarar N81.8bn da kamfanin ya yi a shekarar 2022.
Asarar ta shafi bankuna
A ɓangaren bankuna kuma, FBN Holdings masu bankin First Bank, sun yi asarar da ta wuce N350bn a shekarar 2023.
Kamfanin HoldCo, a cikin watanni uku na ƙarshen shekarar 2023, ya tafka asarar N253.7bn.
A dunƙule kamfanonin bakwai sun yi asarar jimillar kuɗi har N1.7tr saboda faɗuwar darajar naira.
Dangote ya samu riba mai yawa
A wani labarin kuma, kun ji cewa kamfanin simintin Dangote ya samu ribar biliyoyin kudade a ƙarshen shekarar 2023 da ta gabata.
Kamfanin simintin ya sanar da samun riba har naira biliyan 455.58 wanda hakan ke nufin ƙarin kaso 19% idan aka kwatanta da shekarar 2022.
Asali: Legit.ng